Qatar za ta karbi bakuncin Gasar Kofin Asiya ta 2023
Koriya ta Kudu da Indonesia na daga cikin wadanda suka yi zawarcin neman daukar nauyin gasar inda a karshe Qatar ta samu.
Hukumar Kwallon Kafa ta Asiya ta ce kasar Qatar ce za ta karbi bakuncin Gasar Cin Kofin nahiyar ta 2023 bayan China ta fice daga gasar a farkon wannan shekarar saboda matsalar COVID-19.
A watan Yuni 2019 China ta samu damar karbar bakuncin gasar, amma ta fice a watan Mayu, saboda dalilai masu nasaba da yaki da COVID-19.
- Hukumomin da ake neman rushewa sun samu N226bn a kasafin 2023
- Jirage marasa matukan Rasha sun yi wa Ukraine ruwan bama-bamai
“A yau, Kwamitin Zartarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Asiya (AFC) ya tabbatar da Hukumar Kwallon Kafa ta Qatar (QFA) a matsayin wadda za ta dauki nauyin Gasar Cin Kofin Asiya ta 2023,” in ji hukumar.
Da farko an so gudanar da gasar a birane 10 na China a cikin wata daya, daga 16 ga Yuni zuwa 16 ga Yuli na 2023.
Ficewar da China ta yi ya sanya hukumar kwallon kafar shiga laluben kasar da za ta maye gurbinta wajen daukar nauyin gasar.
Koriya ta Kudu da Indonesia na daga cikin wadanda suka yi zawarcin neman daukar nauyin gasar inda a karshe Qatar ta samu.