Qazamen PDP ne suka sa Buhari ya ci zabe – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya soki Jam’iyyar APC a kan yadda take cewa duk ’yan PDP masu cin hanci da rashawa ne, inda ya ce barayi da kazaman jam’iyyarsa ta PDP ne suka kafa gwamnatin Jam’iyyar APC. Alhaji Sule Lamido wanda ya bayyana haka a tattaunawarsa da sashin Hausa na BBC, a […]

Qazamen PDP ne suka sa Buhari ya ci zabe – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya soki Jam’iyyar APC a kan yadda take cewa duk ’yan PDP masu cin hanci da rashawa ne, inda ya ce barayi da kazaman jam’iyyarsa ta PDP ne suka kafa gwamnatin Jam’iyyar APC.

Alhaji Sule Lamido wanda ya bayyana haka a tattaunawarsa da sashin Hausa na BBC, a shekaranjiya Laraba ya ce, an shafe shekaru Jam’iyyar APC tana takara a kasar amma ba ta samu nasara ba sai da “Wadannan barayi kazaman ’ya’yan PDP suka koma suka yi wa APC ciki, sannan aka haifi gwamnatin APC ta yanzu.”

Ya kara da cewa: “Duk masu cewa ’ya’yan PDP barayi ne, to ai ga shi nan barayin ne suka je suka yi cikin wannan gwamnatin har aka samar da ’yar barauniya. Don haka domin da ya zagi uwarsa mene ne laifi?” Ya ce, yana mamakin yadda domin kawai a baya mutum yana Jam’iyyar PDP sai ya koma APC sai a rika ganin kamar ya zama wani waliyyi. “Ga misali lokacin da Atiku yake APC duk an yi shiru, amma yanzu da ya dawo PDP sai aka aka fara zaginsa. A tsarin ’ya’yan APC babu siyasa sai fushi da gilla da cin mutunci babu maganar sanin kasa,” inji shi.

Alhaji Sule Lamido kuma ya ce ba ya fargabar dawowar tsohon Mataimakin Shugaban Qasa Atiku Abubakar cikin Jam’iyyar PDP, kuma dawowarsa ba za ta kawo cikas ga burinsa na tsayawa takarar Shugaban Qasa a shekarar 2019 ba.

Alhaji Sule Lamido ya ce yana maraba da dawowar Atiku cikin PDP domin dama can jam’iyyar ce ta haife shi. “Abin da aka yi wa Atiku Abubakar na daukaka da karamci a PDP ba a yi masa irinsa a APC ba, don haka mene ne laifi don ya dawo gida?” in ji Lamido.

Da aka tambaye shi ko dawowar Atikun ba ta dagula masa lissafi ba? Sai ya ce: “Babban burinmu PDP ta tsayar da dan takara nagari wanda ’yan Najeriya ke so, don haka babu wani abin damuwa, a takaice ma so nake duk ’ya’yan PDP da suka fice su dawo, tunda dai Atiku ya dawo.” 

“So nake su Wamakko su Kwankwaso su AbdulFatah su Saraki su Abdullahi Adamu, su dawo kuma na tabbata za su dawo. Ya kamata a gane cewa su wadannan mutanen duk sun samu sunansu da kwarjininsu ne a PDP. Komawarsu APC cin mutuncinsu ne, wulakanta su ne kuma cin mutuncin tarihinsu ne,” inji shi.

Dawowar Atiku Abubakar, Jam’iyyar PDP a baya-bayan nan, ta sa masu sharhi na ganin za a kai ruwa rana a tsakaninsa da Sule Lamido domin a bayyane take cewa Atiku ya koma jam’iyyar ce domin neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.