Quncin rayuwa ga ma’aikatan gwamnati
Tabbas maganar da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar da wasu gwamnoni suka kai masa ziyara abun dubawa ce! Wasu daga cikin gwamnonin sun shaida masa cewa wai ko albashin sun kasa biya da sauran haqqoqin ma’aikatan jihohin su! A al’ada irin ta ma’aikatan gwamnati babban makamin da suke amfani da shi wajen yakar gwamnati shi […]
Tabbas maganar da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar da wasu gwamnoni suka kai masa ziyara abun dubawa ce! Wasu daga cikin gwamnonin sun shaida masa cewa wai ko albashin sun kasa biya da sauran haqqoqin ma’aikatan jihohin su!
A al’ada irin ta ma’aikatan gwamnati babban makamin da suke amfani da shi wajen yakar gwamnati shi ne yajin aiki! Shi kuwa yajin aiki yana azabtar da su kan su ma’aikatan da sauran talakawa (wadanda ba ma’aikata ba), ke nan su manyan jagorin jiha idan ba su da tausayi kusan zance babu ta inda yajin aikin ke shafar su.
A cikin yan kwanakin na an samu gawar wani ma’aikaci a rataye kansa a bisa dalilin riqe masa albashi da gwamnatin Jihar Kogi ta yi na tsawon wata takwas!
Haka zalika hawan jini da ciwon suga ya kashe mutane da dama musamman tsofaffin ma’aikata da suka yi ritaya. Amma haqqoqin su na fansho da giratuti ya kasa fitowa daga gwamnonin jihohi,
Rashin biyan haqqoqin ma’aikata ya taka rawa sosai wajen tabarbarewar karatun yayansu. Domin idan gwamnati ta rikewa ma’aikaci kudi sai dai a koro yayan su daga makaranta, Hakama rashin biyan haqqoqin ma’aikata ya kai ga har an samu rabuwar aure ba adadi. Ni shaida ne a nan Jihar Zamfara a samu rabuwar aure da dama duk sanadin rike haqqoqin ma’aikata da gwamnati ke yi.
A nan Jihar Zamfara an shiga yajin aiki na kusan mako biyu, An dakatar da wannan yajin aikin ne bayan da wasu daga cikin dattawan jihar suka zauna da wakilan gwamnati. Sai dai ga dukkan alama har yanzu ba’a kama hanyar magance komawa yajin aikin ba, Domin kusan duk alqawuran da gwamnati ta dauka tare da wakilan qungiyar qwadago da dattawan jihar Zamfara ba’a kama hanyar cika su ba!
Abun mamaki da takaici ga halaiyar wasu gwamnonin ita ce shin wai ina kudin da Shugaba Buhari ya basu daga rarar kudin Paris da Landan Club??
Ina suka kai kudin ne, Koko dai sun biya buqatun kawunan su da kudin maimakon amfani da su wajen biyan haqqoqin ma’aikata! Ba ma’aikatan jiha ba har na kanan hukumomi na fuskantar riqewar haqqi, Kasancewa gwamnatin jiha ce keyin uwa tayi makarbiya a wajen tafiyar da harkokin qaramar hukuma, Wani abun tausayi ga ma’aikatan Qananan Hukumomin Jihar Zamfara shi ne har yanzu qaramin albashi ana biyan naira dubu bakwai da rabi biyar!
Dan Allah tayaya wadanda yan kudin za su gamshi ma’aikaci har ya ciyar da kansa da iyalansa da sauran hidimomi? Shawara ta shugaba Muhammadu Buhari ita ce yakamata ya kafa kwamiti mai karfi tare da jagorancin mutanen masu gaskiya su binciki yadda aka kashe kudaden da ka baiwa jihohi. Domin sanin ko kwalliya ta biya kudin sabulu. Lallai tauna wannan tsakuwar zai sanya aya taji tsoro.
Allah ya yi wa ma’aikata tare da daukacin talakawan kasar mu Najeriya mafita.
Za a iya tuntubar Ibrahim Rabilu Tsafe jihar Zamfara. 07064282182