Qungiyar Click 4 help kids ta raba tallafin kayan makaranta ga marayu

A ranar Asabar da ta gabata ce Qungiyar Click 4 help kids ta sauka a Jihar Kano inda ta bayar da tallafin kayayyakin karatu ga dalibai marayu da marasa qarfi. Daga cikin kayyyakin da qungiyar ta raba akwai jakar makaranta da littattafan rubutu da man shafawa da takalma da man goge baki da burushi da […]

Qungiyar Click 4 help kids ta raba tallafin kayan makaranta ga marayu
Qungiyar Click 4 help kids ta raba tallafin kayan makaranta ga marayu

A ranar Asabar da ta gabata ce Qungiyar Click 4 help kids ta sauka a Jihar Kano inda ta bayar da tallafin kayayyakin karatu ga dalibai marayu da marasa qarfi. Daga cikin kayyyakin da qungiyar ta raba akwai jakar makaranta da littattafan rubutu da man shafawa da takalma da man goge baki da burushi da sabulun wanka da sauransu, inda yara dubu 1500 suka amfana.

A jawabin maraba, Ko’odinetar qungiyar ta Afirka Hajiya A’isha Abubakar Aliyu ta ce qungiyar wacce wani dan asalin qasar Brazil mai suna Duoba Braga ya kafa tana tallafa wa yara ne a bangaren ilimi a duniya baki daya, “Qungiyar ta zabi tallafa wa harkar ilimi ne lura da muhimmancin da ilimi ke da shi ga dan Adam. Muna so mu ga cewa maraici ko talauci bai hana kowane yaro samun ilimi ba, don haka muka yunqura wajen ganin an tallafa wa yaran nan da abubuwan da suke buqata wajen neman ilimi,” inji ta.

Ta ce ba wannan ne karo na farko da qungiyar ta fara rabon tallafin a qasar nan ba, ta bayyana cewa sun gudanar da irin wannan tallafi a Abuja inda kimanin yara 6500 suka samu tallafi. “Bayan Abuja mun yi a Kaduna, a yanzu kuma ga shi muna Kano. Za kuma mu je jihohin Gombe da Akwa Ibom don raba wa yaran tallafin. Bayan nan kuma za mu je wasu qasashen Aifrka da suka hada da Kenya da Afirka ta Kudu don bayar da tallafin,” inji ta

A jawabin Kwamishinar Al’amuran Mata da Walwalar Qananan Qara ta Jihar Kano, Hajiya ’Yardada Maikano Bichi ta ce tallafin da qungiyar ta raba ga yaran ya zo a daidai lokacin da ake buqata “Wannan tallafin ya zo a daidai domin yanzu lokaci ne na komawar dalibai makaranta bayan hutu da suka yi. Haka kuma ya zama sauqi ga iyayen dalibai lura da yanayin tattalin arziki da ake ciki don haka iyaye sun samu sauqi.”

Hajiya ’Yardada ta gode wa qungiyar tare da fatan qungiyar za ta ci gaba da bayar da makamancin wannan tallafi ga yaran da ke fadin jihar.