Ra’ayi: Aikin hako fetur na Kolmani jazaman ne —Aliyu Tilde
“Duk wata fargaba da muke da ita a kan dorewar aikin yanzu ta kau”
[Kwanaki] mun halarci wajen kaddamar da shiri na aikin hakowa, sarrafawa da kuma sayar da man fetur na Kolmani. Waiwaiwai! Dadi kashe ni, inji ’yan Hausa fin.
Ina farin cikin sanar da ’yan uwana ’yan Najeriya cewa duk tsoron da muka nuna a baya game da dorewar abun an wuce wurin. Alal hakika ma don warware matsalolin da muka ambata a rubutuna na shekaranjiya ne aka dau lokaci tsakanin 2019 zuwa yanzu.
Tsoronmu na yanda za a kai shi teku, ko a sarrafa shi a nan, ko wani shugaban ya tsaida aikin da na nemo wasu rijiyoyin nan gaba duk an warware su.
Tabbaci
A kan batun tabbacin ci gaba da farautar fetur a kan tudu, da farko dai dokar PIA ta ware 30% na ribar NNPC musamman don haka. Jazaman.
Na biyu kuma, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ba da tabbacin in Allah ya ba shi mulki zai ci gaba da wadannan ayyuka. Tabbaci kuma wanda daga yanda fuskar da ya fade shi ta nuna, da gaske yake yi. Ah. Ko ba komi sai mutanensa sun fi mu morar ayyukan tunda su ke da kudin zuba jari. Don haka ya tsayar da ayyukan ma asara ce, sai dai idan zai yanke hancinsa ne don ya bata wa fuskarsa rai, in ji Turawa.
Sauran ’yan takara ma ya kamata mu ji nasu.
Kudi
Na farko dai kamfanin SEEPCO, wanda shi zai yi aikin haka da sarrafawar, kamar yanda shugansa, Mista Mohit Barot ya ce, ya riga ya tanadi kudi lakadan, watau suna nan a jibge, wanda ake bukata na aikin. Tun da na ji haka na ce, “Af! Aikin gama ya gama.” Sai shukura.
Matatar Mai
SEEPCO zai gina matatar mai a kusa da rijiyar, inda za a rika:
1) Tace har ganga 120,000 na fetur a wuni daya.
2) Samar da gas 500,000 cubic meters a wuni daya
3) Tashar samar da lantarki ta gas din mai karfin 300MW
4) Takin zamani tan 2,500 (buhu 50,000 a wuni daya.
Shagali
Tabdi jam. Gaskiya a gaya wa Baba, ko Arewa ba mu yi sharholiya ba za mu yi shagali, in sha Allahu. Sai dai ya yi hakuri. Ehe. 😁
Dr. Aliyu U. Tilde
Bauchi
23 ga watan Nuwamba, 2022