RA’AYI: Haba Kashim Shettima!
“Wannan kalami na Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima babban abin kunya ne da kuma Allah wadai”
A zabubbukan bana da ba a jima da kammala su ba a Najeriya, sanin kowa ne addini ya taka muhimmiyar rawa sosai. Jam’iyyu biyu Labour Party (LP) da APC su ne suka fi amfani da addini sosai wajen yakin neman zabe.
Mun gani, kuma mun ji yadda dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi da masu mara masa baya suka yi amfani da addinin Kirista a Kudu da Arewa ta Tsakiya wajen yakin neman zabe, wanda wannan salon yakin zaben ya yi tasiri matuka musamman a yankin Kudu maso Yamma da ke da yawan Musulmi, domin galibin masu zabe a yankin sun yi watsi da Tinubu duk da kasancewarsa Beyarbe dan yankin, suka zabi Peter Obi na Jam’iyyar LP saboda addini.
- BIDIYO: An yi jana’izar mutumin da ’yan bindiga suka kashe tare da ’ya’yansa 4
- ’Yan Boko Haram sun kashe manoma 15 a Borno
Wannan ya sa Tinubu ya sha mummunan kaye a jiharsa ta Legas, saboda jihar na da baki masu yawa musamman Ibo da suke kasuwanci, kuma kusan su ne suka fi fita zabe a Legas. Duka unguwanni da akayi zabe aka samu kuri’u masu yawa unguwannin baki ne ’yan ci-rani musamman Ibo, wadanda su ba su cika komawa garuruwansu na asali don jefa kuri’a ba. Sabanin mutanen Arewa da galibi idan lokacin zabe ya zo da yawa sukan komo gida Arewa domin su jefa kuri’a ga dan takarar da suke muradi.
Amma ga ’yan yankin Kudu maso Gabas ba haka abin yake ba, su duk inda suke zaune suke kasuwanci da wahala su koma garuruwansu na asali don yin zabe. Wannan ya sa Ibo da suka yi wa Jihar Legas mamaya ta fuskar kasuwanci, ta kubuce wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben da ya gabata. Haka jihohi irin su Ogun da Osun duk in aka duba za a samu addini ya yi tasiri matuka wajen zaben Shugaban kasa, haka nan yankIn Tsakiyar Najeriya, musamman jihohin Filato da Nasarawa da Taraba da Adamawa da Binuwai da Kogi duka in aka dubi sakamakon zaben Shugaban kasa za a samu addini ya yi tasiri matuka.
Domin bayanai sun nuna cewa dan takarar Jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi ta zagaya manyan coci-coci a Arewa domin kira ga ’yan uwansa Kiristoci su zabe shi Shugaban kasa a zaben da aka yi, wanda wannan ne ya ba shi damar samun kuri’u masu yawa a zaben.
Haka kuma, mun ga yadda malamai a kan mimbarorin Juma’a da wuraren wa’azi da taruka da wuraren da ake gabatar da Ta’alim musamman a tsakanin Sallar Magriba da Isha aka rika yi wa ’yan siyasa yakin neman zabe. Kuma, mun ga yadda da yawan ’yan siyasa suka rika bin malamai a gidajensu da wuraren karatunsu, suna rokon a zabi ’yan takararsu, musamman batun ’yan takara biyu Musulmi, wato Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima.
Wannan na daga cikin hudubobin da aka rika yi wa Musulmi a Arewa a kan su zabi wadannan ’yan takara a matsayin cewa su ne mafita ga Musulmi da mutanen Arewa baki daya.
An yi zargin cewa gwamnoni a Arewa sun yi ta bin gidajen manyan malamai don su jawo hankalinsu su sa a zabi dan takararsu na Shugaban kasa wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kuma da dama daga cikin malaman sun karbi wannan kiran musamman irin su Sheikh Sani Yahaya Jingir inda karara ya rika kiran magoya bayansa su tabbatar sun zabi tikitin Musulmi da Musulmi a zaben Shugaba kasa.
Shi kuma Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum ya ce ya ji ya gamsu Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa ne zabinsa a cikin ’yan takarar, wannan ya so farraka tsakanin malaman da ba sa ra’ayin ’yan takarar Shugaban kasa da Mataimakinsa Musulmi da sauran. Sakamakon amfani da addini da aka yi a zaben ya sa shi da kansa dan takarar Mataimakin Shugaban kasa na APC Alhaji Kashim Shettima ya rika bibiyar gidajen malamai a Kano da Katsina da Kaduna da Bauchi da Sakkwato yana kiran lallai su shiga cikin wannan lamari domin abin nasu ne.
Wanda kuma a zahiri abin a bayyane yake cewa ana yin amfani da addini ne kawai don a samu biyan bukata ba domin an amince bil hakki idan an yi nasara za a taimaka wa addini ko za a fifita muradun addini a gwamnatin ba.
Abin ya zama tamkar yaudara ce kawai, tun da duk wanda ya yi nasara zai rantse ne cewa zai kare Kundin Tsarin Mulki kuma zai yi masa biyayya sau-da-kafa. Dalilin amfani da addini da aka yi a zaben, ya sa kusan har aka zo makon zabe masu hasashe sun gagara gane jam’iyyar da za ta yi nasara a zaben Shugaban kasa a tsakanin manyan jam’iyyu uku PDP da APC da LP.
Domin kowace ka auna nauyinta da yawan magoya bayanta d yadda take tasiri sai ka fahimci cewa za ta iya cin zaben Shugaban kasa, wannan ya faru ne sabanin abin da aka saba gani a baya, inda zabe kan nuna jam’iyyu biyu ne a kan gaba, amma bana sai aka samu jam’iyya ta uku wadda ita ma za ta iya kaiwa ga nasara.
Babban abin mamaki kuma abin kunya da ya faru a makon jiya shi ne, yadda aka ruwaito Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima yana cewa a shugabancin Majalisar Dattawa za su goyi bayan Kirista dan Kudu komai lalacewarsa ko da kuwa akwai Musulmi daga Arewa wanda kwarewa da gogewarsa sun fito fili.
Wannan kalami na Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima babban abin kunya ne da kuma Allah wadai, domin shi da suka yi amfani da sunan addini suka ci zabe bai kamata a ji yana kware baya ga addinin da don shi aka zabe shi ba. Cewa da Musulmi dan Arewa gara Kirista dan Kudu babban cin mutunci ne ga al’ummar Musulmi da kuma Arewa.
A nan ya kamata dukkan malaman duk suka yi uwa, suka yi makarbiya a kan a yi zaben addini su fito su yi Allah wadai da kalaman Mataimakin Shugaban kasar na nuna cin fuska ga Musulmi game da Shugabancin Majalisar Dattawa.
A zaben Shugaban kasa sun yi amfani da addini sun ci zabe, amma a zaben Shugaban Majalisar Dattawa sun yi watsi da addini bil hasali ma sun yi bakaken maganganu ga addini domin kawai samun biyan bukatarsu.