RA’AYI: Tsakanin Kano da Lagos

Daga Suleiman A Suleiman Masana Tattalin Arziki na da wani tsari da suke kira Hasken Dare. Wato adadin  hasken da ake iya gani a birni, ƙasa, ko nahiya ta hanyar hotunan satilayit da aka ɗauka da daddare. Masanan na amfani da wannan hasken a matsayin ma’aunin alƙaluman tattalin arziki irin su ƙarfin arzikin da ƙasa […]

RA’AYI: Tsakanin Kano da Lagos

Daga Suleiman A Suleiman

Masana Tattalin Arziki na da wani tsari da suke kira Hasken Dare. Wato adadin  hasken da ake iya gani a birni, ƙasa, ko nahiya ta hanyar hotunan satilayit da aka ɗauka da daddare. Masanan na amfani da wannan hasken a matsayin ma’aunin alƙaluman tattalin arziki irin su ƙarfin arzikin da ƙasa ke samarwa, talauci, bambancin dake tsakanin mai shi da mara shi, samuwar kayayyakin more rayuwa, da sauransu, musamman a ƙasashe da nahiyoyin duniya da ba a tattara ingantattun alƙaluma.

Shahararren misalin wannan tsarin shi ne yadda ake kwantanta hasken dare tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa; Kudu  cikin haske tarwai yayin da Arewa ke cikin duhu dunɗum, abinda ke nuna bambancin tattalin arzikin dake tsakanin ƙasashen biyu. Kodayake hoton sataliyet yafi nuna Hasken Dare dalla-dalla, ko da idonka ka leƙo ta tagar jirgin sama yayin sauka da daddare kana iya ganin bambanci a zahiri. Duk wanda ya taɓa gwada haka ya san bambancin dake tsakanin hasken dare a Lagos da na Kano ya isa misali: ɗaya na cikin haske wasai yayin da ɗayan sai dai ka hango hasken jefi-jefi.

Hasken Dare a Lagos bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da Johannesburg, Singapore, Dubai ko London. Amma abinda nake son nunawa shi ne hasken dare, kamar kanun labarai, adadin kuɗaɗen da ake tarawa a cikin gida, adadi da salon kaɗa ƙuri’a, yawan yaran da suke zuwa makaranta, ƙaruwar yawan al’umma, da sauransu, zai iya haska mana alƙibla da ci gaban jihohi biyun da suka fi yawan jama’a a Najeriya. Kanun labarai daga jihohin biyu a makon jiya sun isa misali.

A Lagos, babban labarin shi ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da layin jirgin ƙasa na cikin gari mai suna Red Line, wanda a cewar Gwamna Babajide Sanwo-Olu zai yi jigilar fasinja 500,000 a kullum. A Kano, labari ake na Hisba, wata hukumar kula da tarbiyya, da ta kasa samun gurbin zama a hukumance ko a aikace, ko kuma samun  tasiri a cikin al’umma. Amma baya ga Hasken Dare da kanun labarai sai mun dubi yadda jihohin ke kallon kansu, tsarin siyasarsu, da kuma ingancin shugabancin da suka samu tun daga 1999 domin mu fahimci tazarar ci gaban da ake samu tsakanin Lagos da Kano.

Akwai kamanceceniya sosai a tsakaninsu. Duk suna da muhimmin tasiri a siyasar Najeriya. Su ne jihohin da suka fi yawan al’umma da kuma ƙabilu dabam-dabam. Mai yiwuwa ne ma Kano ta fi Lagos yawan nau’in ƙabilu. A nan zaka ga jikokin ƴan Yemen, Syria, Lebanon, Afirka ta Arewa, Chad, Mali, Nijar, da ƙabilun Kanuri, Yoruba, Nupe, Edo, da ma wasu da dama, balle a zo batun Fulani da sauran Hausawa da suka zama halattattun Kanawa, masu harshe ɗaya, aƙida ɗaya sanadiyyar tsawon zama da auratayya tsakaninsu. Ƙabilun da suka zama ƴan gari a Lagos ba su kai na Kano ba kuma a shekarun 1970, ana iya cewa  Kano ta zarta Lagos wurin zama cibiyar masana’antu. Sai dai jihohin biyu sun ɗauki turbobin da suka saɓa da juna matuƙa gaya.

A 1999, Lagos ta ɗauki kanta a matsayin cibiyar tattalin arzikin Najeriya kuma shugabanninta suka ɗau hanyar da za su ƙara ƙaimi a wannan ɓangare. Tun a  1999 suka fara maganar samar da wutar lantarki ta su ta kansu, samar da manyan motocin sufuri, jirgin ƙasa na cikin gari, wadatar da al’umma da gidaje, tashar jiragen sama a tsibirin Lagos, Babbar Gada ta huɗu, da kuma mayar da unguwannin matalauta dake tsakiyar birnin zuwa halattattun cibiyoyin kasuwanci.

Kawo yanzu basu cimma waɗannan manufofin ba, amma tinƙis-tinƙis suna kan hanya, yayinda gwamnoni ke ɗorawa daga inda magabatansu suka tsaya tare da bunƙasa tattalin arzikin jihar aƙalla idan aka kwatanta da sauran jiohin Najeriya, koda a wasu lokutan hakan  na sa jihar ta yi taho-mu-gama da gwamnatin tarayya. Tsarin siyasa da shugabancin da suka bi shi ma ya taimaka wurin cimma waɗannan manufofi koda kuwa a kan yi zargin mutum ɗaya ne ke juya akalar jihar. Amma dai tsarin ya biya buƙata, kuma sakamakon ya bayyana a zahiri, koda kuwa da sauransu idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.

Amma labarin ya sha bamban a Kano. A 1999, babu wanda yake kokwanton Kano ce cibiyar tattalin arzikin Arewacin Najeriya, kuma ta biyu ga Lagos a faɗin ƙasar nan. Sai dai a farkon shekarun 2000 sai alƙiblar ta fara sauyawa. A yanzu ita ce ta takwas a samun kuɗin shiga cikin jihohin Najeriya, yayinda Lagos ta riƙe kambunta har ma ta ƙara tazarar dake tsakaninta da sauran jihohi. Don kuwa maimkon Kano  ta gina kanta a matsayin cibiyar kasuwanci ta Arewa kuma ta biyu a Najeriya, sai ta nemi ta zama “jihar da tafi Musulunci a tsakanin jihohin Musulmin Arewacin Najeriya”, ko me hakan ke nufi a Najeriyar da dama fiye da rabinta Musulmi ne?

Maimakon a kalli sufuri a matsayin wata hanyar inganta harkokin kasuwanci sai aka ɗauke shi a matsayin wani nauyi na addini, domin samun damar hana maza da mata cakuɗa a cikin abin hawa, ta hanyar samar da  babur mai ƙafa uku da aka raɗawa sunan da ya dace da shi na “Adaidaita Sahu”. Wato maimakon a yi tunanin sababbin hanyoyin da za a shigar da mata cikin harkokin kasuwanci, kamar yadda Turkey, Indonesia da sauran ƙasashen Musulmi suka yi, sai aka ga zai fi kyau a ƙara killace su daga idon jama’a da kuma harkokin kasuwancin. Kuma maimakon aci albarkacin damar da harshen Hausa ya bayar na zama harshen Yammacin Afirka, a fitar da abubuwan gargajiya zuwa kasuwannin duniya, sai aka ɓuge da kafa Hisbah da Hukumar tace Finafinai.

Bugu da ƙari, yayin da siyasar Lagos ke da manufa a jiha da tarayya, Kano ta na gudanar da siyasa da take cikin waɗanda suka fi rashin samar da riba a Najeriya. A duk zaɓuɓɓukan shugaban ƙasa tun daga 1999, mutanen Kano suna tuttuɗo ƙuri’un da suka nunka na Lagos, sai dai jagororin jihar ba su gano yadda za su yi amfani da wannan damar su kawo mata cigaba ba, sai dai samarwa waɗansu ƴan tsirari muƙaman siyasa.

Siyasar cikin gida ma tafi haka lalacewa. Daga washegarin ranar zaɓe har zuwa jajiberin zaɓe mai zuwa bayan shekaru huɗu, kullum mutane na shiga gidajen rediyo suna fafatawa a fagen siyasa a madadin wani ubangidansu, akan wani abu maras amfani. Babu wani waje a faɗin Najeriya da ake tattauna siyasa akai-akai kamar Kano, amma ba sa  haifar da komai sai dai gadar sama a nan, gadar ƙasa a can: abinda ya zama tsarin samar da kayan more rayuwa da sauran jihohi Arewa suke kwaikwaya. Mutane uku ne suka mulki Kano daga Mayu 1999 zuwa Mayu 2023. Amma zazzafar adawar dake tsakaninsu da tsakanin magoya bayansu, da kuma yadda kullum ake bayyanar da wannan adawar, sun jawo babu abinda ake samu a Kano face siyasar rashin cigaba ko kuma ace siyasar surutu don dai ace an ce.

Sai dai, har yanzu Kano na fuskantar ƙalubalen haɓaka zuwa tsarin tattalin arziki na zamani: wutar lantarki ta kan ta, haɓaka sufuri, wadatar da al’umma da gidaje, ƙarin ƙwararrun mutane da ayyukan ƙwararru, da kuma dawo da masana’antu ta yadda za su yi kan-kan-kan da rukunonin shaguna. Haka kuma akwai ƙalubalen dawo da martabarta a matsayin cibiyar bunƙasar tattalin arziki ta Arewa; da kuma siyasa mai manufa da shugabanci nagari don samun wannan sauyin da ake buƙata.

A mataki na farko, ya zama wajibi ga shugabannin Kano su kawo wani sabon tsarin siyasa mai sauƙin kace-nace da kuma manufar haɓaka tattalin arziki, ta tsawon aƙalla kimanin shekaru 25, wadda duk gwamnatin da aka zaɓa ita za ta bi, kuma a kanta za ta jagoranci mutane ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba. Abu na biyu, ya zama wajibi Kano ta samo hanyar da zata ci gajiyar ɗimbin ƙuri’un da take kaɗawa a siyasar ƙasa wurin janyo tallafin gwamnatin tarayya domin ci gaban jihar, da kuma ɗabbaƙa manufar jihar ta bunƙasa masana’antu, alal misali. Na uku, kuma mafi muhimmanci, wajibi ne jihar Kano ta ɗora ɗimbin kasuwancin da ake yi a cikinta bisa tsari na zamani domin samun ƙarin haraji da kuɗin shiga ga gwamnatin.

Duk waɗannan abubuwa ne masu yiwuwa amma akwai buƙatar abubuwan da suka zarta Hukumar Hisba da baburan Adaidaita Sahu.

 

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe