Ra’ayi: Yadda talla ke sanadin lalacewar ’ya’ya mata a Arewa

Mafiya yawan yaran da ake lalatawa, sune ’yan talla.

Ra’ayi: Yadda talla ke sanadin lalacewar ’ya’ya mata a Arewa

Illolin yin talla ga ’yan mata  (1)

Na yanke shawarar yin wannan rubutu ne bayan lura da na yi da abubuwan da ke faruwa na yau da kullum, musamman a cikin anguwannin mu, kauyuka da birane. Sannan a matsayina na mace kuma uwa, na ga bai dace na yi shiru ba.

Domin kuwa addini ya koyar da mu idan muka ga mummuna mu gyara shi da hannunmu, ko da baki, ko kuma idan mu da rauni sosai mu ki abin a zuciyarmu kawai, mu kawar da kai.

Ko da yake ba zan iya daukar matakin hanawa ko tsawatar wa iyaye masu dora wa yaransu talla ido da ido ba to, amma zan yi amfani da damar da nake da ita, a matsayina na marubuciya, don in fadakar da duk wanda Allah Ya sa ya ga wannan rubutu nawa, domin shi ma ya isar gaba. Don kuwa ba zan iya shiru in kawar da kai ba.

Da yawan mutane sukan yi kokari don ganin sun tserar da mutuncin kansu da na iyalinsu daga gudun fadawa cikin abin kunya. Amma ba kasafai suka cika damuwa da halin da iyalin makwaftan su da wasu daban za su shiga ba. Kamar ta karin maganar Malam Bahaushe ne da ke cewa, ‘Idan jifa ya wuce kan ka, kan uban kowa ma ya fada!’ Subhanallah!!

Mafiya yawan yaran da ake lalatawa, sune ’yan talla, kuma mun san akasari rashi da talauci ne ke sa iyaye su dinga dora wa yaransu kayan sayarwa suna yawo da shi gida gida ko kwararo-kwararo, duk da kuwa su ma ba a son ransu hakan ke faruwa ba sai don ba yadda za su yi ne. Sai dai kuma idan muka duba ta wata fuskar, akan samu iyaye marasa godiyar Allah, wadanda ke da rufin asirin da za a iya cewa sun fi karfin duk wani abin da za su ci ko su sha, amma hakan ba isa ba, dole sai sun sa yaransu sun yi talla, abin da sau da dama yake janyo wata babbar matsala daga bisani.

Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne, rashin daukar kwakkwaran mataki akan masu aikata irin wannan laifi, duba da yadda rayuwa ta canza, abubuwa suka dada lalacewa. Rashin daukar mataki ya sa da yawa iyaye masu aikata wadannan laifuka suke cigaba da aikatawa ba tare da sanin cewa suna aikata wani kuskure na zubar da kima da mutunci, da jefa rayuwar yaro ko yarinya cikin hadari ba.

Wasu ’yan mata masu talla

Daga cikin hadarin da talla ke jefa rayuwar karamin yaro ko budurwa shi ne yiwuwar shiga hannun bata-gari, masu lalata yara ta hanyar fyade ko yaudara. Wannan shi ne yake sa yarinya ta taso da budadden ido ko shiga wani mawuyacin hali, wani lokaci ma har da shaye-shaye. Ko a addinin Musulunci ma sam sangarta yaro da masa rikon sakainar kashi hakan bai kamata ba, ballantana barin abin da zai yi wa rayuwar sa illa ya taba shi.

Saboda lalacewar zamani, jahilcin iyaye da cin hanci da rashawa da ya yi katutu a zukatan wasun mu, da wuya ka ga an hukunta masu irin wannan mummunan laifi na fyade, saboda dalilai na shari’a, rashin ba da hadin kan ’yan uwa da iyaye wajen bin diddigin shari’a don tabbatar da ganin an hukunta wanda ya yi wa ’yar su ko dan su fyade, da koya musu halayen banza. Shi ya sa ake ganin yawanci masu aikata wanan laifi suna samun daurin gindi, daga manya da shugabanni ko kuma bayar da cin hancin dan kar a hukunta su, abin da yake mayar da kasar mu baya.

Abin bakin ciki ne da mamaki ka ga uba ya lalata ’yar da ya haifa, wa’iyazubillah! Sannan kuma wasu iyayen rashin sa ido a kan ’ya’yan su shi ne ke sa har yarinya ko yaro su sauka a kan layi, ma’ana su fara lalacewa, ba tare da sun sani ba, saboda ko dai uwar tana fita dillanci da neman kudi, ko yawace-yawacen gidajen kawaye da ’yan uwa, uba kuma ya fita nema tun safe bai dawo ya waiwayi yadda rayuwar yaran ta wuni ba. Irin wannan ke lalata tarbiyyar iyali da haifar da wata mummunar matsala da za a yi da na sani a kanta.

Ko da yake ba za a rasa iyaye masu sa ido suna bibiyar rayuwar iyalinsu da shigi da ficen su. Ana samun iyaye mata da za ka ga suna iya kokarinsu wajen gani sunn killace ’ya’yanta, amma babu yadda ta iya domin kaddara ta riga fata.

Wasu yaran sukan ji tsoron fada wa iyayen su halin da suke ciki da kuma barazanar da suke samu daga masu aikata musu hakan, duk kuwa da illar da hakan yake yi ga rayuwar su. Ya kamata iyayesu rika samun lokaci suna kusantar ’ya’yans’u, suna sanin halin da suke ciki.

A cikin garin Jos an taba samun wani uba da ya lalata yaransa uku. Amma abin takaici babu wani mataki da aka dauka a kansa na hukunci, kuma a dalilin hakan zai sa masu niyyar aikata hakan su kara jin kwarin gwiwar aikata hakan,  sabanin in aka yi hukunci. Bayan nan ma kuma tsoro zai darsu a zuciyar sa da sauran mugayen iyayen da suke  aikata, don gudun hukuncin da zai biyo bayan su.

Ya zama dole iyaye mata da maza kara sa ido matuka a kan yaransu mata har ma da maza baki daya, domin yanzu rayuwa ta zama sai addu’a.

A karshe ina mai shawartar iyaye da mu tashi tsaye mu dage da yi wa yaran mu tarbiyya ta gari, ba su ilimi mai inganci, dora su a tafarkin addini, da nisan ta su daga duk wani abin da zai iya zubar musu da kima da mutunci ko ya jefa su cikin wata mummunan rayuwa.

Ayar Alkur’ani ta umurce mu da mu tseratar da kawunan mu da iyalan mu daga wata wuta wacce makamashinta mutane ne da duwatsu!

Allah ya tsare mutuncin mu da imanin mu, ya kuma bai wa kasar mu zaman lafiya, shugabannin mu Allah ya ba su hikima da basirar jagoranci cikin adalci da gaskiya, ta yadda za a kawar da barna da shimfida jagoranci nagari.