RA’AYIN AMINIYA: Wajibi ne ASUU da Gwamnatin Tarayya su fifita bukatun dalibai

Aminiya na kira ga bangarorin biyu su mayar da wukake cikin kube

RA’AYIN AMINIYA: Wajibi ne ASUU da Gwamnatin Tarayya su fifita bukatun dalibai

Wakilan Gwamnatin Tarayya da na ASUU yayin wata tattaunawa

Fiye da wata shida ke nan da kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta tsunduma yajin aiki, inda ta fara da na mako hudu domin matsa wa gwamnati lamba ta biya musu bukatunsu, sai dai kuma kafiya da rashin jajircewa daga bangaren gwamnati da kungiyar sun hana cim ma matsaya domin kawo karshen yajin aikin.

Gwamnati da kungiyar ASUU sun kasa fahimtar halin da iyayen yara da dalibai suke ciki da kuma muhimmnacin bukatar samar wa matasa ilimi mai nagarta. Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu, inda ta bukaci a sake tattaunawa a kan matsayar da ta cim ma da Gwamnatin Tarayya a shekarar 2009 da maye gurbin hanyar biyan albashi ta IPPIS da UTAS da biyan alawus-alawus na malaman da tallafa wa jami’o’i da kudade da bayyana rahoton kwamitin ziyarar jami’o’i da ya kammala aikinsa a bara da kuma samar wa jami’o’i mallakar jihohi kudade. kungiyar ASUU ta yi kaurin suna wajen yin yajin aiki.

A shekara 13 da suka gabata, kungiyar ta tafi yajin aiki sau tara, inda a lokacin mulkin Shugaba Buhari kawai ta shiga yajin aiki sau biyar. kungiyar ASUU ta tsunduma yajin a lokacin kowace gwamnati tun daga 1992.

Wato kimanin shekara talatin ke nan tana ci gaba da yajin aiki, amma yar yanzu an kasa warware matsalolin, ga shi kuma tsarin jami’armu da rayuwar daliban Najeriya da ma ita kanta kasar na shiga mawuyacin hali. Baya ga dalibai na bata lokaci kafin su kammala karatunsu saboda yawan tsaikon da ake samu sakamakon yajin aikin, wanda yake matukar illata manyan makarantun Najeriya.

Haka kuma, yajin aikin ya haifar da samar da dalibai marasa nagarta, domin kuwa iyayen da suke da abin hannu suna kai ’ya’yansu jami’o’i masu zaman kansu a kasar nan ko a kasashen ketare, wadanda suka hada da kasashen da ake da shakku a kan tsarin jami’o’insu, kawai saboda dalibai sukan kammala karatunsu a kan kari. Jami’o’in gwamnati sun fara zama tamkar firamare da sakandaren gwamnati, inda ake bambance su ba wai ta fuskar ingancin koyo da nazari ba, sun zama matattarar ’ya’yan talakawa da marasa galihu.

Duk da haka, maimakon su yi kokarin cim ma matsaya a tsakaninsu, Gwamnatin Tarayya da kungiyar ASUU sun buge da yin farfaganda da ba ’yan Najeriya bayanan karya. Misali, a ranar 17 ga Agustan 2022, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya sanar da ’yan Najeriya cewa, an warware duk wata matsala da ke tsakanin gwamnati da kungiyar ASUU, illa kawai biyan albashin watannin da kungiyar ta yi a yajin aiki, inda ya ce gwamnati ba za ta biya ba domin hakan ya zama izina ga masu niyyar shiga yajin aiki. Ministan ya kara ba wa dalibai shawara su kai kungiyar ASUU kotu bisa bata musu lokaci da ta yi.

A daya bangaren kuma, kungiyar ASUU ta karyat acewa, ba ta taba tattauna matsalar albashin baya da Ministan ba, inda ta ce ba a cim ma yarjejeniya ba a kan muhimman batutuwan da suka haifar da fara yajin aikin. Haka kuma ta kudiri aniyar ci gaba da yajin aikin da ba a san karshensa ba. A fili yake babu kyakkyawar niyya a tattaunawar, domin kuwa kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ba su dauki hanyar shawo kan matsalar ba. Wannnan ba daidai ba ne kuma bai dace ba.

Dole bangarorin biyu su sassauta. Gwamnatin Tarayya ba ta nuna cikakkiyar jajircewa ba wajen aiwatar da rahotannin kwamitocin sasantawa ba, wato Kwamitin Farfesa Munzali Jibrin na watan Mayu, 2020 da kuma na baya-bayan nan na Farfesa Nimi Briggs, wanda aka kaddamar da shi a farkon fara yajin aikin.

Tabbas, kowane bangare na kokarin yi wa bangaren ilimin kasar nan kisan mummuke, inda suke nuna halin-ko-in- kula. Baya ga nuna gazawa da Gwamnatin Tarayya da kungiyar ASUU suka yi wajen kawo karshen yajin aikin, dole ne bangarorin biyu su daina nuna wa juna gadara, domin kuwa babu wani dalili na yin yajin aikin har wannan tsawon lokaci.

Dole ne su sa bukatun kasa a gaba a yayin da suke yanke shawara. Haka dole ne bangarorin biyu su fahinci cewa, Najeriya ba za ta iya yi wa bangaren ilimi rikon sakainar kashi ba, domin kuwa ilimi shi ne yake bayyana yadda kasa za ta kasance a nan gaba da kuma irin al’ummar da za su zo nan gaba. Don haka, duk wata shawara da za a yanke, dole ne a sa bukatun kasa a kan gaba.

Jaridar Aminiya na kira ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace wajen ganin an kawo karshen yajin aikin da yake yi wa rayuwar matasa barazana. Ya kamata Shugaba Buhari ya shiga maganar da kansa ba wai ya wakilta Minista ba. Ita kuma kungiyar ASUU ya kamata ta fahimci cewa, ba fa kowa ne yake samun yadda yake so ba, sannan su dinga duba abin da zai yiwu dangane da walwalar malaman da kuma ba jami’o’in kudi a kasar nan.

Haka lokaci ya yi da Majalisar Dokoki ta kasa da Majalisar kasa da tsofaffin shugabannin kasa da sarakunan gargajiya da shugabannin addini su shiga wannan magana domin ganin an kawo karshen yajin aiki da kuma nemo bakin zaren. Saboda haka, bai kamata a bar kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya kawai a cikin maganar ba.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano