Ra’ayoyin jama’a kan tsarin takaita amfani da kudi
A ranar Talatar makon jiya ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci a fara aiki da tsarin takaita amfani da tsurar kudi a dukkan fadin kasar nan. An fara amfani da wannan tsarin ne a ranar 1 ga Janairu, 2012, don a takaita yawaita amfani da tsurar kudi a hannun jama’a, don kuma a rika karfafa […]
A ranar Talatar makon jiya ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci a fara aiki da tsarin takaita amfani da tsurar kudi a dukkan fadin kasar nan.
An fara amfani da wannan tsarin ne a ranar 1 ga Janairu, 2012, don a takaita yawaita amfani da tsurar kudi a hannun jama’a, don kuma a rika karfafa amfanin da harkokin cinikayya da ajiyar kudi ta hanyar zamani.
An fara amfani da wannan tsarin ne a Jihohin Kano da Ogun da Legas da Anambara da Abiya da Ribas da kuma birnin Abuja. A yanzu kuma an ci gaba da amfani da wannan tsarin a sauran jihohi 30 da suka rage.
Wannan tsari na takaita amfani da tsurar kudi ya bayyana cewa, idan har mutum zai cire tsurar kudi ko kuma ajiye tsurar kudin da ya fi Naira dubu 500, to za a caje shi, haka ga asusun kungiya ko kuma na hadin-gwiwa kada ya wuce Naira miliyan 3.
Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da wannan sabon tsarin na takaita amfanin da tsurar kudi.
Abdullahi Abubakar Lamido Malami a Jami’ar Jihar Gombe kuma mai sharhi kan tattalin arzikin kasa ya ce tsarin ya dace, zai taimaka wa gwamnati wajen rage yawan kudin da take kashewa don buga takardun kudin da kuma na ajiyarsu bayan an buga.
Alhaji Fatai ya ce sabon tsari yana da kyawu musamman ma idan aka duba matsalar tsaron da Najeriya ake fama da ita. daukar kudi niki-niki a fili shi ke jawo hankalin barayi.
Ya ce burinsa a samar da wadatacciyar hanyar sadarwa ga dukkan bankunan kasar nan, kasancewar yin hakan zai sanya tsarin ya samu tagomashi a wurin jama’a.
Sunday Banike ya ce ba tun yanzu ya kamata a kawo wannan tsarin ba, domin yawo da kudi cikin aljihu na tattare da hadari.
“Idan na yi maka aiki ban cika son ka ba ni kudi ba, ina da injin POS, idan kana da katin banki sai ka sanya shi a ciki, ni kuwa in cire kudin aikina.” Inji shi.
Aminu Muhammad Migini mai sayar da atamfa a babbar kasuwar Gombe ya ce rashin kyawun sadarwa (network) a kasar nan ba zai bar wannan tsarin ya yi tasiri ba.
Ya ce ci gaban da ake da shi a Najeriya bai kai a kawo wannan tsari ba, saboda kamfanonin layin sadarwa suna da matsala a kasar nan.
Ahmad Ibrahim Sulaiman ya ce ya yi amfani da wannan sabon tsarin kuma ya ji dadinsa, amma babbar matsalar wannan tsarin shi ne, ba kowane wuri ke da na’urar biyan kudi na tsarin rashin takaita yawo da tsurar kudi ba.
Jafar Ilyasu Chiromawa mai buga bulo ya ce wannan sabon tsarin yana da amfani, musamman ma wajen saukaka hanyoyin cinikayya. Matsala daya ita ce, ta rashin tsayayye kuma ingantaccen layin sadarwa.
Rabi’u Shitu Kandahar ya ce ya yi shekara 4 yana amfani da wannan tsarin, domin a da yakan yi tafiya dauke da kudi, sai ya rika tunanin kada ya yasar da su ko kuma kada a sace, amma yanzu a huldar da yake yi da kamfani, kai tsaye kawai yake biya ko a biya shi.
Ya ce sai dai ana fama da matsalar yawan daukewar layin sadarwa.