…Ra’ayoyin ‘yan majalisar Amurka kan sallamar Tillerson
Wakilin Aminiya a Amurka ya rairayo ra’ayoyin ’yan Majalisar Dokokin Amurka kan sallamar Red Tillerson da Shugaba Trump ya yi. Jim kadan da sanarwar cewa an sallami Tillerson, sai sanatoci da dama musamman masu fada-a-ji da ’yan Majalisar Wakilai suka shiga bayyana ra’ayinsu kan wannan mataki da Shugaban Amurkar ya dauka. Da yawan wadanda Aminiya […]

Wakilin Aminiya a Amurka ya rairayo ra’ayoyin ’yan Majalisar Dokokin Amurka kan sallamar Red Tillerson da Shugaba Trump ya yi.
Jim kadan da sanarwar cewa an sallami Tillerson, sai sanatoci da dama musamman masu fada-a-ji da ’yan Majalisar Wakilai suka shiga bayyana ra’ayinsu kan wannan mataki da Shugaban Amurkar ya dauka. Da yawan wadanda Aminiya ta jiwo ra’ayinsu sun yaba ne wa tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurkar Red Tillerson.
Da yawan ’yan Jam’iyyar Republican da suke rike da mukamai a Majalisar Dattajawa sun goyi bayan sauyin tare da cewa za su tabbatar sababbin da za a nada sun tsallake tantancewar da za a yi musu a majalisar.
Su kuma ’yan Jam’iyyar Democrats sun bayyana kin amincewarsu da matakin na Shugaba Trump, musammam a kan wadanda ya bayyana za su maye gurbinsu wato Mike Pompeo da Gina Haspel, wadanda ga dukan alamu za a samu takun-saka wajen tantantace su.
Shugaban Majalisar Wakilai, Paul Ryan na sahun gaba cikin masu goyon bayan matakin, inda ya bayyana Mike Pompeo a matsayin reza sarkin kaifi, kuma agogo sarkin aiki, ya ce ba shakka ba a yi zaben tumun-dare ba, sannan ya ce yana taya Gina Haspel murna kan sabon mukaminta domin ita ce mace ta farko a tarihi da ta taba rike wannan mukami.
Sanata Bob Corker daga Jihar Tennnessee kuma Shugaban Kwamitin Harkokin kasashen Waje ya ce sallamar Tillerson ya zo masa da mamaki kwarai da gaske.
Sanata John Corny na Jam’iyyar Republican daga Jihar Tedas ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Pompeo zai tsallake tantancewar da Majalisar Dattawan za ta yi masa.
A lokacin da aka nada shi Shugaban Hukumar CIA, an jefa masa kuri’a 51 na goyon baya yayin da 49 ba sa goyon bayansa, shi ya sa wadansu ke ganin akwai kallo idan an zo batun tantance shi a wannan karo.
Sanata Richard Burr daga Jihar Arewacin Korolina kuma Shugaban Kwamitin Hukumar Leken Asiri cewa ya yi yana fatar ganin ya goyi bayan zaben da aka yi wa Gina Haspel a matsayin Daraktar Hukumar CIA, ya ce tana da dimbin basirar da za ta iya wannan aikin domin ta dade a cikinsa.
Sanata John McCain na Jam’iyyar Republican kuma tsohon dan takarar Shugaban Amurka duk da ba ya zauren majalisar yana Jihar Arizona inda ake masa jinyar kwakwalwa ya ce akwai bukatar Haspel ta zo ta yi bayani kan rin rawar da ta taka a cikin shirin binciken da hukumar ke yi game da tuhumar da ake yi a kan wadansu ’yan ta’adda da ke gidan fursunan Guntanamo Bay a kasar Kyuba har ma da sauran inda ake tsare da ’yan ta’adda a duniya.
Sanata Ron Wyden na Jihar Oregon ana bayyana sunayen mutanen biyu ya sa kafa ya yi fatali da lamarin, inda ya ce Pompeo ya nuna son rai sannan ya yi sakwa-sakwa da batun binciken da ake yi ga Rasha, ya ce wani lokacin ma bayanansa suna karo da juna. Da kuma yake sharhi a kan Haspel sai ya ce muddin aka ce yau wannan matar ita ce Shugaban Hukumar CIA, to gwamnatin ba ta da sauran damar cewa zat a rufe wasu abubuwa game da ayyukan asshan da ta aikata a wani lokaci can baya.
Jakadar Amurka a Majalisar dinkin Duniya, Nikki Haley ta bayyana zaben Pompeo a matsayin wata babbar nasara ga Gwamnatin Shugaba Trump