Ra’ayoyin ’yan Najeriya kan tashin Matatar Warri

Wasu ’yan Najeriya sun bayyana shakku kan fara aikin Matatar Man Fetur ta Warri da Kamfanin NNPC ya sanar

Ra’ayoyin ’yan Najeriya kan tashin Matatar Warri

Bayan da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya sanar da dawowar aikin Matatar Man Fetur ta Warri da ke Jihar Delta, ’yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.

A yayin da wasu daga cikinsu suke bayyana farin cikinsu, wasu kuma sun bayyana shakku a kan lamarin musamman a shafukan sada zumunta.

Tashin Matatar Warri na zuwa ne ƙasa da wata biyu bayan da Matatar Mai ta Fatakwal  ta koma bakin aiki.

Matatar, wadda aka dakatar da aikinta a shekarar 2015 domin gudanar gyare-gyare, ta ci gaba da aiki, inda aka fara tace man fetur.

Komawa aikin matatar zai rage dogaro da man fetur da ake shigo da shi daga ƙasashen waje da kuma bunƙasa harkar mai da iskar gas a Najeriya kamar yadda Kamfanin NNPC ya bayyana.

Wasu daga cikin ’yan Najeriya sun bayyana ra’ayinsu game da wannan yunkuri na NNPC, inda suke ganin dole a yaba wa kamfanin bisa yadda suka jajirce a kan yadda matatunmu na gida ke farfaɗowa daga doguwar suma da suka yi.

Sanusi Ibrahim ɗan Najeriya ne wanda yake ganin cewa dawowar aikin matatun a yanzu nasara ce ga gwamnatin Tinubu idan aka kwatanta da shekarun da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya kwashe yana son gyaran matatar kamar yadda ya bayyana a sashin tsokaci bayan fitar labarin dawowar aikin matatar.

“Wallahi Baba Buhari ya ji kunya, shekara takwas ya kasa gyara su duk da alƙawarin da ya yi, amma ga shi cikin ƙasa da shekara biyu Tinubu ya gyara su.” In ji shi.

Shi kuwa Rabi’u Haruna Bagari cewa ya yi: “… tun a baya ba su gyara ba sai da suka ga Dangote ya buɗe tashi don kawai su rage masa riba. To Alhamdulillah Allah Ya sa su amfane mu baki ɗaya. Allah Ya sa Najeriya ta gyaru.”

Haka kuma a ɓangare guda kuma akwai masu fatan matatar su ɗore da aiki ba kamar yadda wasu ke zargin cewa matatar Fatakwal ta tsaya da aiki kwanaki kaɗan daga dawowarta aiki.