Raba geron kunu a masallatai ba hakkin gwamnati ba ne – Ambasada Jumba

Ambasada Muhammed Jumba, tsohon Jakadan Najeriya ne a kasar Kuwait, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce da raba geron kunu da wasu jihohi ke yi a masallatai ba hakkin gwamnati ba ne: Ka gamsu da yadda Shugaba Buhari ke tafiyar da Najeriya? Tabbas zan iya cewa na gamsu da yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake […]

Raba geron kunu a masallatai ba hakkin gwamnati ba ne – Ambasada Jumba
Raba geron kunu a masallatai ba hakkin gwamnati ba ne – Ambasada Jumba

Ambasada Muhammed Jumba, tsohon Jakadan Najeriya ne a kasar Kuwait, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce da raba geron kunu da wasu jihohi ke yi a masallatai ba hakkin gwamnati ba ne:

Ka gamsu da yadda Shugaba Buhari ke tafiyar da Najeriya?
Tabbas zan iya cewa na gamsu da yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake tafiyar da Najeriya, domin lokacin da ya karbi ragamar shugabancin kasar nan abubuwa da dama ba sa tafiya daidai. Ya samu dimbin matsaloli kuma babbar nasarar da aka samu a gwamnatinsa ita ce zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hakika mutane suna fama da talauci da tsadar rayuwa, kayan abinci ya yi tsada a kasuwannin kasar nan, sakamakon barnar da aka yi ne a baya muke shan bakar wahala a yanzu. Amma muna fata ’yan Najeriya za su ci gaba da ba shi dukkan goyon bayan da ya kamata domin shugabanci abu ne mai matukar wahala.
Yaushe kake jin ’yan Najeriya za su yi ban-kwana da talauci?
Allah ne kawai zai iya magance talauci da tsadar rayuwa a tsakanin jama’a ba Shugaba Buhari ba, akwai abinci a Najeriya, sai dai babu kudin saye ne. Kasuwannin kasar nan da shaguna a cike suke da kayan abinci abin da yake wahala shi ne kudin saye. 
Kana ganin matakin da gwamnati ta dauka na hana shigo da shinkafa ya dace?
Ban san lokacin da Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da shinkafa daga kasashen waje ba, abin da na sani shi ne matukar ana rage shigo da kayan abinci daga kasashen waje kayan abincinmu na gida zai yi daraja a kasuwannin duniya.
Mene ne ra’ayinka kan sunayen sababbin jakadu 47 da aka aika wa majalisa domin tantancewa?
A matsayina na tsohon Jakadan Najeriya a kasar Kuwait wadanda aka aike da sunayensu zuwa ga majalisa sun san yadda ake aikin jakadanci. Abin da zan fada musu shi ne su zamo mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana sannan su guji cin hanci da rashawa domin Shugaba Buhari mutum ne wanda ba ya son rashawa a rayuwarsa.
Mene ne sakonka ga matasan Najeriya?
Babban sakona ga matasan Najeriya da na Jihar Bauchi baki daya shi ne su dage sosai wajen neman ilimin addini da na zamani, domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba da bunkasar tattalin arziki sai da matasa masu ilimi. kasashe da dama suna tanadi ga matasa domin su ne shugabannin gobe sabanin yadda muke a Afirka. Ina kira da babbar murya ga gwamnonin kasar nan su yi wa Allah su biya ma’aikata da ’yan fansho hakkokinsu duk da cewa mun san ana fama da karancin kudi a wasu jihohin Najeriya. Kuma ina kira ga kowa ya zamo mutumin kirki mai gaskiya da rikon amana irin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin ta haka ne za mu samu ci gaba a kasar baki daya, shi kadai ba zai iya gyara Najeriya ba kowa ya yi gaskiya shi ne mafita. 
Me za ka ce game da tsagerun Neja-Delta masu fasa bututun mai?
Abin da zan fadi shi ne ya kamata gwamnati ta fito da wasu sababbin dabaru na tattaunawa da tsagerun domin ba na kaunar su ci gaba da fasa bututun mai da kudin mai ake biyan albashi a jihohin Najeriya.
Amma kuma ya kamata a fahimci cewa ko ba man fetur Najeriya za ta rayu muna da dimbin gonaki da dabbobi da sauran albarkatun kasa.
Kana goyon bayan a sauke wasu daga cikin ministocin da ba sa kokari?
Yaushe aka rantsar da su da har za a fara maganar Shugaba Buhari ya sauke wadansu daga cikin ministocin da ba sa kokari? Amma idan Shugaban kasa ya ga akwai wadanda ba sa kokari wuka da nama na hannunsa tunda shi ne ya zabe su. Ina tabbatar maka cewa duk ministan da ya ci kudin talakawa a wannan gwamnati, to, tabbas Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sauke shi kuma ya gurfanar da shi a gaban kotu.
Ka je kasashen duniya sun kai nawa?
Maganar gaskiya na je kasashe masu yawa a duniya kuma na ga abubuwa wadanda ba zan taba mantawa ba a rayuwata. Misali na je kasar Amurka da Ingila da Kuwait da Saudiyya da sauransu, akalla na je kasashen duniya sama da 25.
Me za ka ce game da gwamnatin Jihar Bauchi da ta gagara raba geron kunu a masallatai kamar yadda aka saba duk shekara?
Raba geron kunu a masallatai ba hakkin gwamnati ba ne, duk gwamnatin da take raba geron kunu a masallatai ta saki hanya, domin ba an zabi Gwamna ya raba gerun kunu ba ne, abin da muke son Gwamna ya yi, ya samar da tsaron rayuka da dukiya, ya gyara hanyoyin da suka lalace, ya samar da magunguna a asibitoci da sauran ayyukan raya kasa.
Masallatan da ake raba musu geron kunu nawa ne a Jihar Bauchi, wadanda ake ba su ba su da yawa, zalunci ne a dauki masallatai 50 a raba musu geron kunu a bar sama da masallatai dubu goma babu komai. Zamanin mulkin su Sardauna da Tafawa balewa ba sa raba geron kunu a masallatai, sun yi mulki lafiya har gobe ana ci gaba da yi musu addu’a kuma ka bincika babu inda Sardauna ya raba geron kunu a masallatai a zamanin mulkinsa. Limaman da suke huduba a kan an hana su gerun kunu ya kamata su fahimci cewa abin da ake yi musu a shekarun baya zalunci ne karara. Limamai ne ya kamata su fada wa gwamnati gaskiya, dukiyar gwamnati ta kowa da kowa ce, a rika raba wa ga wadansu mutane ’yan kalilan a cikin al’umma zalunci ne babba ya kamata limamai su fahimci haka. Idan aka gyara hanyoyi da kudin geron kunu kowa zai amfana domin mutane da dama za su bi hanyar su kuma yi addu’a ga gwamnati.
A karshe mene ne sakonka ga gwamnatin Jihar Bauchi?
Babban sakona ga gwamnatin jihar Bauchi shi ne ta tabbatar duk wanda ya yi aiki an biya shi albashinsa, duk da cewa sun ce kudin da suke samu ya kasa sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya, muna fata Allah Ya kawo kudin da za a biya ma’aikata albashinsu. Sannan su ma ma’aikata su ci gaba da hakuri, tunda kowa ya san halin da ake ciki a kasar baki daya.

Daga Hamza Aliyu, Bauchi