Rabaran Iloh ga Jonathan: Kada ka tsaya takara a badi

Babban Shugaban Cocin Soul Winning Chapel da ke Ebute-Metta a Legas kuma Shugaban Iklisiyyar Eclectic Network, Rabaran Moses Iloh, ya shawarci Shugaba Goodluck Jonathan da kada ya tsaya takara karo na biyu a zaben badi.Rabaran Moses Iloh ya bayyana haka ne a wata budaddiyar wasika da ya aike ga Shugaban kasar, inda ya ce yadda […]

Rabaran Iloh ga Jonathan: Kada ka tsaya takara a badi
Rabaran Iloh ga Jonathan: Kada ka tsaya takara a badi

Babban Shugaban Cocin Soul Winning Chapel da ke Ebute-Metta a Legas kuma Shugaban Iklisiyyar Eclectic Network, Rabaran Moses Iloh, ya shawarci Shugaba Goodluck Jonathan da kada ya tsaya takara karo na biyu a zaben badi.
Rabaran Moses Iloh ya bayyana haka ne a wata budaddiyar wasika da ya aike ga Shugaban kasar, inda ya ce yadda harkokin siyasa suke tafiya a yanzu abin damuwa ne, kuma ana nufin wargaza Najeriya.
Ya bayyana yadda fasalin siyasa da mulkin Najeriya ke tafiya da abin takaici da tsabagen rashin sanin ya kamata da rashin imani da bakin zalunci, yana mai cewa alamu sun fara nuna cewa idan ba a zabi Jonathan a karo na biyu ba, zai kasance babu Najeriya.
“Ka same mu a matsayin dunkulalliyar Najeriya, duk da cewa kasar tana fama da matsala…Amma yadda harkokin siyasa suke tafiya a yanzu abin tsoro ne, kuma babu abin da suke nunawa ban da niyyar wargaza kasar nan. Shugaban kasa: Ina rokonka da kada ka tsaya takara a zaben 2015. Ka riga ka zama Shugaban kasa, idan ka zama tsohon Shugaban kasa za a ci gaba da martaba ka har karshen rayuwarka. Kuma za ka zama abin misali nagari ga ’yan siyasa saboda gagarumar gudunmawar da ka bayar wajen tabbatar da dorewar kasarka Najeriya,” kamar yadda wasikar ta bayyana.
Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa limamin ya ce zamanin mulkin Jonathan ya ba da fiffiko da karrama munafukai da marasa tsoron Allah da miyagun mutane da suka samu shiga gwamnatinsa a matsayin manyan masu ba shi shawara, inda ya kara da cewa alhali babban burin wadannan miyagu ita ce tara kazantacciyar dukiya da wargaza kasar ta hanyar neman karin shekara hudu domin cimma muguwar manufarsu.
Sai ya bukaci Shugaba Jonathan ya yi koyi da salon shugabanci na Yesu Almasihu, yayin da ya tunatar da masu muguwar manufa a kasar nan su sani cewa Allah Yana nan, kuma Shi ne Mai gudanar da al’amuran duniya.