Rabida za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da masu fakewa da addini suna ta’addanci

Shugaban Majalisar Musulunci ta Duniya (Rabida) Sheikh Abdallah Ben Abdel Mohsen At-Turki, ya bayanan jin dadinsa kan yadda ya ga Musulmin Najeriya suke gudanar da harkokinsu na Musulunci a kasar nan, inda ya ce majalisar da kuma kasar Saudiyya za su taimaka wa Najeriya wajen yaki da miyagun akidu da ake fakewa da Musulunci ana […]

Rabida za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da masu fakewa da addini suna ta’addanci
Rabida za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da masu fakewa da addini suna ta’addanci

Shugaban Majalisar Musulunci ta Duniya (Rabida) Sheikh Abdallah Ben Abdel Mohsen At-Turki, ya bayanan jin dadinsa kan yadda ya ga Musulmin Najeriya suke gudanar da harkokinsu na Musulunci a kasar nan, inda ya ce majalisar da kuma kasar Saudiyya za su taimaka wa Najeriya wajen yaki da miyagun akidu da ake fakewa da Musulunci ana aikata ta’addanci kamar yadda ’yan ta’addar Boko Haram ke yi.
Sheikh Abdallah At-Turki ya zo Najeriya ne don halartar taro kan sahihiyar akidar Musulunci da wanzar da zaman lafiya da aka gudanar na hadin gwiwar Ahlus Sunnah, a karkashin jagorancin Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau a Abuja.
Sheikh Abdallah At-Turki ya ce ta hanyar komawa ga koyarwar Alkur’ani da Hadisin Manzon Allah (SAW) ne za a iya yaki da wannan fitina ta ’yan ta’adda da ke addabar kasashen Musulmin daban-daban.
Jakadan Saudiyya a Najeriya, Fahad bin Abdullah, ya ce Najeriya na cikin gamayyar kasashen Musulmi 34 da Saudiyya za ta jagoranta domin yaki da ta’addanci. Haka kuma ya ce ta’addancin ’yan kungiyar ISIS da sauransu da ke barazana ga zaman lafiyar kasashen, abu ne da ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.