An nada Gwamna Inuwa Yahaya Matawallen Kaltungo
Mai martaba Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad, ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya da sarautar Matawallen Kaltungo. Tabbacin Wannan sarauta ta Matawallen Kaltungo, tana dauke ne a wata takarda da Mai Kaltungo ya aiko wa Gwamnan wacce tsohuwar Kwamishinar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Hajiya Sa’adatu Sa’ad Musthapha ta gabatar masa. Sarkin […]
Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe
Mai martaba Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad, ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya da sarautar Matawallen Kaltungo.
Tabbacin Wannan sarauta ta Matawallen Kaltungo, tana dauke ne a wata takarda da Mai Kaltungo ya aiko wa Gwamnan wacce tsohuwar Kwamishinar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Hajiya Sa’adatu Sa’ad Musthapha ta gabatar masa. Sarkin ya ce al’ummar Kaltungo suna jin dadin yadda Gwamnan yake nuna musu kauna wajen ayyukan raya kasa wannan ya sa suka kara masa kwarin gwiwa wajen ba shi goyon baya da addu’o’i.
Da yake karbar sarautar Gwamna Inuwa Yahaya, ya gode wa Mai Kaltungo bisa wannan karamci da ya nuna masa sai kuma ya yi alkawarin ci gaba da tafiyar da ’yan uwantakar da ke tsakaninsu da al’ummar Kaltungo da daukacin jama’ar jihar. Ya ce ya san wannan sarauta ta Matawalle tana da muhimmanci, don haka yana tabbatar musu da cewa zai rungume ta hannu bibiyu kamar yadda ya rungumi sarakuna iyayen kasa.