‘Rabin kaso’

Assalamu alaikum Manyan gobe. Yaya shirin komawa makaranta? Tare da fata nana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan “Rabin Kason”. Labarin ya yi nuni ga sakamakon karbar cin hanci. A sha karatu lafiya. Taku: Amina  Abdullahi. An yi wani attajiri wanda yake shirin karbar  bakinsa daga wani gari. Attajirin […]

‘Rabin kaso’

Assalamu alaikum Manyan gobe. Yaya shirin komawa makaranta? Tare da fata nana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan “Rabin Kason”. Labarin ya yi nuni ga sakamakon karbar cin hanci. A sha karatu lafiya.

Taku: Amina  Abdullahi.

An yi wani attajiri wanda yake shirin karbar  bakinsa daga wani gari. Attajirin ya dauki alkawarin shiryawa bakin nasa liyafar tande-tande  don haka, sai ya yanke shawarar sanya masu aikinsa da su girka duk irin nau’ukan abinci masu dadi. 

Bayan ma’aikatan sun gama girka abincin sai suka tuna wani abinci wanda ake yin sa da kifi. Sun nemi kifi duk fadin garin ba su samu ba. Rashin samun kifin ya sanya attajirin ya yi sanarwar bada babban kaso ga wanda ya kawo masa kifi a gidansa.

Labarin sai ya isa kunnen wani mai sayar da kifi. Da ma bai cika rasa kifi a gidansa ba. Sai ya dauki babba daga cikin kifin ya isa gidan attajirin amma maigadi ya hana shi shiga wai sai ya dauki alkawarin ba shi rabin kason da zai samu daga wajen attajirin.  Mai kifi ya yarda sannan maigadin ya kyale shi ya wuce.

Mai kifi na bai wa attajirin kifi sai attajirin ya nemi ya yi masa kyauta amma ya ki.   Ya ce shi dai yana so ne a yi masa bulala 50 amma yana so a yi masa 25 ne yayin da sauran 25 kuma a yi wa maigadi. A nan ne attajirin ya gane abin da mai kifin yake nufi. Ya sanya aka zane maigadi sannan aka kore shi daga bakin aiki kuma ya yi wa mai kifi kyauta mai yawa.

Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi daga wannan labari.