Rabin maniyatan Jigawa ba za su je Hajjin bana ba
Ga dukan alamu rabin miniyyata daga Jihar Jigawa ba za su gudanar da aikin Hajjin bana ba, sakamakon gazawar da suka yi wajen cikata sauran kudin kujerarsu bayan da aka bayyana kudin kujerar na Naira miliyan daya da rabi. Wakilinmu ya ce tabbatattun bayanan da ya samu daga Hukumar Alhazai ta Jihar sun ce rabin […]

Ga dukan alamu rabin miniyyata daga Jihar Jigawa ba za su gudanar da aikin Hajjin bana ba, sakamakon gazawar da suka yi wajen cikata sauran kudin kujerarsu bayan da aka bayyana kudin kujerar na Naira miliyan daya da rabi.
Wakilinmu ya ce tabbatattun bayanan da ya samu daga Hukumar Alhazai ta Jihar sun ce rabin maniyyatan ba za su sauke faralin ba ne a bana saboda tsadar kujerun.
Hukumar Hajji ta kasa ta kebe wa jihar kujeru 2,677, amma har zuwa lokacin da wakilimmu ya rubuto wannan labari, maniyyatan da suka iya biyan cikakken kudin kujerar ba su wuce 1,412 kamar yadda Kakakin Hukumar Alhazan ta Jihar Jigawa Malam Ibrahim Salisu Kanya ya tabbatar masa ta waya.
Malam Ibrahim Kanya, ya ce sauran kujerun da ba a cikata kudadensu ba da wadanda
ba a sayar ba za su mayar wa Hukumar Hajji ta kasa ce domin a sayar wa wadanda suke bukata.
Ya ce duk da umarnin da aka bai wa maniiyatan na su cika kudin a kan lokaci hakan ya gagara.
Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Sani Muhammed Alhassan ya ce jihar ce ta fi arahar kujerar aikin Hajji a bana domin wasu jihohin suna sayar da kujera a kan Naira miliyan daya da dubu 600, sabanin jihar da aka samu ragin Naira dubu 100.
Wannan ne karo na farko a tarihin jihar da aka gaza sayar da kujerun aikin Hajji da aka jihar.
A baya gwamnatocin jihar sun rika saye sauran kujerun suna raba wa jama’a tare da kokarin cikata wa wadanda kudinsu ya gaza don su sauke faralin kuma su yi wa gwamnatin jihar da kasa addu’a a can kasa Mai tsarki.
Akwai masu ganin cewa duk da karayar tattalin arziki akwai yiwuwar gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar za ta saye sauran kujerun ko wasu daga ciki domin ta raba wa jama’a, su sauke farali tare da yi wa jihar da Najeriya da kuma Shugaban kasa addu’a.
Malam Ibrahim Salisu Kanya ya ce ana sa ran crwa a ranar 17 ga Agusta ne maniyyatn jihar za su fara tashi zuwa Saudiyya daga filin jirgin saman Dutse.