Rabin mutanen Arewa maso Gabas na da matsalar kwakwalwa —Masana
Kungiyar Likitocin Kwakwalwa ta Najeriya (APN) ta ce matsin tattalin rayuwa ya hana masu fama da matsalar tabin kwakwalwa samun kulawar da ta dace.
Masana lafiyar kwakwalwa sun bayyana cewa kimanin rabin al’ummar Arewa maso GabashinNajeriya na fama da tabin kwakwalwa a sakamkon tsawon lokaci da yankin ke fama da matsalar ta’addanci da ta matsin rayuwa a kasar.
Shugaban shugaban Kungiyar Likitocin Kwakwalwa ta Najeriya (APN) Farfesa Taiwo James Obindo ya ce matsin tattalin arziki ya hana masu fama da matsalar tabin kwakwalwa samun kulawar da ta dace.
Farfesa Taiwo James Obindo ya shaida wa taron kungiyar da ya gudana a Maiduguri cewa rashin tsaro, garkwua da mutane, rashin aiki, kashe musu ‘yan uwa da masoya, da kuma rashin aiki mai kwari.
Sauran sun hada da “ta’ammali da miyagun kwayoyi. Shekarar 2006 kashi 25 cikin 100 ke fama da matsalar, amma matsalar tsaro ta sa abin ya karu a Arewa maso Gabas zuwa kusan kashi 50 na mutanen yankin a tsawon lokacin da yankin ke fama da ta’addnci.
- Farin Magi Mara Alama Na Barazana Ga Lafiyar Al’umma —Masana
- Jerin hatsarin jiragen sojin Najeriya a 2023
Ya ce a aikin kyautar da kungiyar APN ta gudanar kafin taron, likitocin sun duba marasa lafiya 500 a Maiduguri, amma “Da da hali da mutum 5,000 za mu duba.”