Rabon albarkatun kasa ya kara raba kan wakilan taron kasa
Wasu wakilai a wurin taron kasa sun yi bore a shekaranjiya Laraba game da shawarar da shugabannin shiyyoyi suka yanke kan kason da za a rika ba jihohin da ake hako albarkatun kasa daga jihohinsu.Shugabannin shiyyoyin sun ba da shawarar a kara kason jihohin da ake hako man fetur daga kashi 13 cikin 100 zuwa […]
Wasu wakilai a wurin taron kasa sun yi bore a shekaranjiya Laraba game da shawarar da shugabannin shiyyoyi suka yanke kan kason da za a rika ba jihohin da ake hako albarkatun kasa daga jihohinsu.
Shugabannin shiyyoyin sun ba da shawarar a kara kason jihohin da ake hako man fetur daga kashi 13 cikin 100 zuwa kashi 18, yayin da suka ba da shawarar a ba jihohin da ake hako ma’adinan kashi biyar cikin 100, sai kuma kashi biyar na dukiyar kasa ga jihohin Arewa maso Gabas da ’yan Boko Haram suka yi wa kaca-kaca.
Kwamitin shugabannin shiyyoyin da ya hadu da wakilan kungiyoyin mata da na kare hakkin jama’a da na kwadago da na matasa ya mika rahotonsa ne ga zauren taron a shekaranjiya Laraba. Kuma taron ya dage zamansa kafin lokacin tashinsa domin bayar da damar yin muhawara kan rahoton a jiya Alhamis.
Wakilan Kudu maso Kudu da na Kudu maso Gabas da kuma na Kudu maso Yamma sun ki amincewa da shawarwarin inda suka sha alwashin za jefa kuri’ar rashin amincewa da shi a zaman na jiya. Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba mu samu sakamakon zaman na jiya ba.