Rabon Awaki bai dace da Gwamnan Kano ba — Jaafar Jaafar
Ya zama dole mu gaya wa Gwamnan gaskiya saboda mun tallata wa mutane shi da tunanin cewa daban yake da saura.
Fitaccen ɗan jaridar nan Jaafar Jaafar ya ce bai dace Abba Kabir Yusuf da kansa ya je rabon akuya ba yana matsayin Gwamnan Kano.
A ranar Talata ce Gwamnan dai ya yi rabon jajayen awaki da wilbaro da nufin tallafa wa mata da matasa da jari domin dogaro da kansu.
- An tsinci gawar magidanci a rijiya a Kano
- ’Yan fashi sun hallaka mutum 7 a harin Kasuwar Ngalda da ke Yobe
Sai dai Jaafar Jaafar a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce sam hakan bai dace ba da matsayinsa na Gwamnan Kano.
Jaafar ya ce kasancewar yana daga cikin waɗanda suka dinga Alla-wadai da makamancin wannan rabon da dan takarar Gwamnan Kaduna Isah Ashiru ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe, ya sa dole a yanzu su fito su soki Abban shi ma.
“Da farko dai akwai abubuwan da bai kamata a ga Gwamna a ciki ba. Daukar mataki guda ɗaya da zai iya tada ƙura ka iya lulluɓe duk wasu matakai masu kyau na kawo ci gaba da dan siyasa ya yi a mulkinsa. Kuma da wancan ɗayan za a ci gaba da tuna shi ko ba ya nan.
“Misali, mun fi tuna tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo kan barnatar da $16bn (bayan $3.55 ne) a harkar gyaran wutar lantarki fiye da gina tashoshin wutar lantarki 10 da ya yi karƙashin shirin NIPP.
“Don haka Gwamna Abba ya kamata ya tuna cewa a karni na 21 muke, lokacin da fasaha ta ƙirƙirarriyar basira AI, motoci da jirage marasa matuƙa, da sauran harkokin fasaha ke tashe.
“Kano kullum na yabon Legas saboda tsare-tsare da shirye-shiryen da ta gina kanta da su, amma idan jagororinmu suka zo da wasu shirye-shiryen sai ka zaci mutanen zamanin da suke mulka.
“Yanzu da ƙananan hukumomi suka samu ‘yancin cin gashin kai, kamata ya yi a bar musu rabon jarin dabbobi da wilbaro.
“Ya zama dole mu gaya wa Gwamnan gaskiya saboda mun tallata wa mutane shi da tunanin cewa daban yake da saura,” in ji Jaafar Jaafar.