‘Rabuwar kawunan Boko Haram alamar karyewarsu ce’

Sanarwar nada Abubakar Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar Boko Haram da kungiyar ISIS ta yi a makon jiya tare da samun baraka ta bangaren wani kusa a kungiyar mai suna Mamman Nur ta haifar da muhawara a tsakanin al’ummar Jihar Borno wadda ta fi fuskantar ta’addancin Boko Haram a tsawon shekara bakwai Malam Umar […]

‘Rabuwar kawunan Boko Haram alamar karyewarsu ce’
‘Rabuwar kawunan Boko Haram alamar karyewarsu ce’

Sanarwar nada Abubakar Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar Boko Haram da kungiyar ISIS ta yi a makon jiya tare da samun baraka ta bangaren wani kusa a kungiyar mai suna Mamman Nur ta haifar da muhawara a tsakanin al’ummar Jihar Borno wadda ta fi fuskantar ta’addancin Boko Haram a tsawon shekara bakwai Malam Umar Muhammad Maizabura, wanda dan siyasa ne kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum ya ce barakar alama c eta nesa ta-zo kusa na ganin bayan kungiyar, “A gaskiya rarrabuwar kawunan shugabannin kungiyar Boko Haram babban alheri ne ga gwamnati da ’yan Najeriya. Na farko yanzu ba su da tasiri sosai saboda sojoji sun karya lagonsu tare da toshe musu hanyoyin samun makamai da abinci da kudi da man fetur da kuma kashe mafi yawa dakarunsu. Na biyu karya lagonsu da aka yi ya haifar da kiyayya a tsakaninsu inda suke zargin juna da rashin yarda da juna har suke kokowar shugabanci a tsakaninsu, ta yadda bangarorin biyu suke zargin shugabancin Shekau. Ya ce, yanzu abin da ya rage shi ne gwamnati ta yi kokarin cin gaba da kutsawa cikinsu ta nemi sulhu da wani bangare ta yadda za a gano sirri da maboyarsu a iya magance su,” inji shi.
 Wani tsohon jami’in tsaro mai suna Malam Ibrahim Goni, cewa ya yi, “Ganin gardama ta barke a
tsakaninsu tare da neman shugabanci wannan ne lokacin da gwamnati za ta iya kutsawa cikinsu a shawo kan wani bangare don a samu a ci lagon sauran. Kada ka manta an kasha akasarin mayakansu kuma an datse hanyoyin samun abubuwan da suke kara musu karfi tare da shiga dajin Sambisa. To wannan nasara da aka samu a kansu na tabbatar da cewa karfinsu ya kare sauran duk abin da za su fada farfaganda ce kawai don nuna suna da tasiri, alhali ba su shi. Idan sojojinmu suka ci gaba da nausawa dajin Sambisa, babu shakka za su gama da su cikin kankanen lokaci.”