Rabuwar Najeriya ba alheri ba ne – Akbishop Kaigama
Akibishop Ignatius Kaigama shi ne Akibishop na darikar Katolika na Jos kuma Shugaban Majalisar Bishop-Bishop din Katolika ta Najeriya. A tattaunawarsa da wakilinmu kan masu kiraye-kirayen a raba Najeriya, ya ce raba Najeriya ba shi ne mafita ba, ya ce al’ummar Najeriya su rike gaskiya shi ne mafita. Kuma ya ce Allah ne Ya sake […]

Akibishop Ignatius Kaigama shi ne Akibishop na darikar Katolika na Jos kuma Shugaban Majalisar Bishop-Bishop din Katolika ta Najeriya. A tattaunawarsa da wakilinmu kan masu kiraye-kirayen a raba Najeriya, ya ce raba Najeriya ba shi ne mafita ba, ya ce al’ummar Najeriya su rike gaskiya shi ne mafita. Kuma ya ce Allah ne Ya sake dawo da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya ci gaba da ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ta shiga:
Aminiya: Me za ka ce kan masu kiraye-kirayen a raba Najeriya da masu neman a sake fasalinta?
Akibishop Kaigama: Zancen a raba Najeriya ba zance ne mai ma’ana ba. Domin Allah ne Ya hada mu wuri daya a matsayin Najeriya, don haka zancen a raba Najeriya bai taso ba. Idan ba mu iya zama tar a Najeriya ba, ko an raba Najeriya gida 30 matsalar da muke da ita a Najeriya za ta ci gaba a sababbin kasashen nana 30, idan aka raba. Don haka idan ana neman gyara ne a Najeriya a yi aiki da gaskiya, idan muna aiki da gaskiya ba za mu samu matsala ba. Idan ana amfani da kudaden da Allah Ya ba mu yadda ya kamata, ba za a ji mutum guda ya kwashe biliyoyin Naira ba. Duk abin da ake da shi za a yi amfani da shi ta yadda zai amfani kowa da kowa, ba za a samu matsala ba.
Ba maganar raba kasa ba ce, zancen a yi gaskiya ce a Najeriya, zancen a yi kwazo kowa ya tsaya ya yi aikinsa tsakani da Allah kan gaskiya ne ake bukata. Idan aka raba Najeriya za a gadar da matsalolin da muke fama da su zuwa ga sabbabin kasashen da za a raba, don haka gara mu ci gaba da zama tare.
Maganar sake fasalin kasar nan yana da kyau, domin idan dan Adam yana raye ya rika sake fasali daidai ne. Amma wane irin fasali ne ake son a sake a Najeriya? Ba dai maganar a raba kasar nan ba. A nemi hanyar da za a yi gyara a yi abubuwan da za su amfani al’ummar Najeriya da kara daukaka rayuwar al’ummar Najeriya ne ake bukata. Idan wadansu suna ganin ana ci musu tuwo a karya ne, suna neman a yi gyara, wannan daidai ne. Amma wai maganar raba kasa ko a tara dukiyar kasa a bai wa sashi daya, wannan bai taso ba. Allah Ya ba mu wannan arziki tare ne. Akwai lokacin da a nan Jos ana hakar ma’adinan karafa,, ana kaiwa kasashen waje ana samun kudaden shiga wadanda aka yi amfani da su a Najeriya baki daya. Yanzu akwai arzikin mai a kasar nan, ya kamata wannan arzikin mai ya amfani kowa da kowa a Najeriya. A raba komai daidai ta yadda kowa zai samu ya amfana. Wuraren da ake hakar mai a kula da su, a ba su abin da za su ci gaba da shi, domin ba su da kasar noma ko kamun kifi a wurarensu, don haka dole a lura da su.
kasarmu Najeriya kasa ce mai albarka kuma Allah Ya ba mu albarkar yawan jama’a. Kwantar da hankali shi ne matsala a Najeriya.Yanzu a Najeriya za ka ji a Gabas akwai matsala a Kudu da Yamma haka suke. Maimakon mu tara hankulanmu mu hada kai mu yi abubuwan da za su taimake mu, mun tsaya muna nuna bambancin kabila da addini. Maimakon wadanda Allah Ya ba su mukamai a kasar nan na shugabanci su nuna alheri su nuna gaskiya su bauta wa jama’a sun kasa yin haka. Don haka muke fama da wahala a kasar nan. Allah Ya ba mu Shugaban kasa mai kwazo da gaskiya, ya kamata kowa ya rike gaskiya a Najeriya tun da Allah Ya ba mu wannan shugaba. Domin Shugaban kasa Buhari yana yin shugabanci na gaskiya a kasar nan. Don haka ina kira ga al’ummar Najeriya mu kwantar da hankalinmu mu yi aiki tare mu manta da maganar bambance-bambance. Idan muka yi haka za mu samu ci gaba a Najeriya, za mu samu nasara fiye da kasashen Turawa.
Aminiya: Me za ka ce game da dawowar Shugaban Buhari daga jinyar da ya je waje da kuma abubuwan da kake ganin ya kamata ya mayar da hankali a kai?
Akibishop Kaigama: Da dawowar Shugaban kasa komai ya canja a Najeriya. A lokacin da yake waje kowa yana ta surutu, amma daga isowarsa duk masu surutu kowa ya yi shiru komai ya lafa. Wannan ya nuna cewa Shugaban kasa Buhari mutum ne mai daraja wanda mutanen Najeriya suke kauna da girmamawa.
Allah Ya dawo da shi lafiya domin ya ci gaba da bauta wa kasar nan. Akwai aikin da Allah Ya bai wa Shugaba Buhari a Najeriya bai yi rabi ba. Ya zo da niyyar gyara a Najeriya amma akwai wadanda ba sa son wannan gyara da yake yi. Suna son a ci gaba da zamba da cuta a Najeriya. Don haka ina kira ga Shugaba Buhari ya kara sanya ido a kan gyaran da ya zo yi a Najeriya. Maganar yaki da cin hanci da rashawa ya rufe ido ya ci gaba da wannan aiki. Ko wane ne ko dan jam’iyyarsa ne ko dan wata jam’iyya ne aka kama da laifi kan wannan al’amari na cin hanci da rashawa ya tabbatar an hukunta shi. Ya samu ya tattara dukan abubuwan da aka sace domin talakawa suna shan wahala a kasar nan. Muna da yara da dama wadanda ba su da aikin yi, a ba su aiki yi.
Wadanda suke tare da shi wato ministoci da masu taimaka masa su zamanto masu gaskiya da rikon amana. Mun tabbata idan Shugaba Buhari ya ci gaba da wannan gyara da ya sanya a gaba za a samu sauki a Najeriya. Dubi irin amfanin gonar da Allah Ya ba mu a daminar bana, duk inda ka duba a jihohin Arewa ga amfanin gona nan ya yi kyau ga shinkafa da masara da dawa nan duk sun yi kyau. Gwamnati ta bude gonaki ta samar wa al’umma taki da irin shuka da taraktocin noma kan farashi mai rahusa.
Aminiya: Wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar kasar nan?
Akibishop Kaigama: Sakona ga al’ummar Najeriya shi ne mu yi kokari mu zama daya, kada mu yarda wani ya rude mu mu rarrabu. Idan muka rarrabu za mu shiga wahala don haka mu yi kokari mu zama daya. Domin a nan Arewa muna da abin da mutanen Kudu suke bukata, a Kudu suna da abin da muke bukata a Arewa. Mu hada kai mu yi amfani da karfi da ilimi da dukiyar da Allah Ya ba mu, idan muka yi haka za mu samu ci gaba a Najeriya, yadda Turawa za su yi fada a kan neman izinin zuwa Najeriya domin su zo su zauna.