Radaman: Yadda za ku sauke Al-Kur’ani cikin sauki

Hanya mafi sauki da za ka sauke Al-Kur’ani a watan Ramadan

Radaman: Yadda za ku sauke Al-Kur’ani cikin sauki

A yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke ci gaba da gudanar da azumin Ramadan, sun kuma himmatu wajen neman kusanci da Allah a cikin watan mai alfarma.

Malamai sun kwadaitar da yawaita ayyukan samun lada musamman karatun Al-Kur’ani, kasancewar a watan ne aka saukar da Al-Kur’ani, sama da shekara 1900 da suka gabata.

Akwai hanyoyin da dama da mai azumi zai iya karance Al-Kur’ani daga bango zuwa bango cikin sauki a watan, gwargwadon yanayinsa.

Mutum zai iya karance shi sau daya a cikin watan idan ya raba karatunsa a tsakanin sallolin na farilla, kamar haka:

Karantu shafi hudu a tare da kowace sallar farilla —shafi biyu kafin sallah, shafi biyu bayan sallar.

Da haka, kullum za ka karanta shafi 20 ke nan, wanda shi ne izu biyu.

Al-Kura’ani yana izu 60 ne a cikinsa, kuma shafukansa kusan shafi 600 ne.

A cikin kwana 30, wanda da bi wannan tsari zai rika karanta shafi 20 kullum na Al-Kur’ani na tsawon kana 30, wand hakan zai ba da shafi 600.

Allah Ya sa mu dace.