Radda ya yi wa Kwamishinoni sauyin ma’aikatu a Katsina

Gwamnatin ya yi sauye-sauyen ne da nufin inganta ayyukan gwamnatinsa.

Radda ya yi wa Kwamishinoni sauyin ma’aikatu a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi wa wasu kwamishinoni sauye-sauyen muƙamai domin inganta ayyukan gwamnatinsa.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar.

A sabon sauye-sauyen, gwamnan ya naɗa Alhaji Malik Anas a matsayin sabon kwamishinan Ma’aikatar Tsare-Tsare da Tattalin Arziƙi.

Malik Anas, ya taɓa riƙe muƙamin Akanta-Janar na Jihar Katsina, kuma memba ne a ƙungiyoyin ƙwararru daban-daban.

A sauye-sauyen, Alhaji Bello Husaini Kagara, wanda a baya yake jagorantar Ma’aikatar Tsare-Tsare da Tattalin Arziƙi, an mayar da shi zuwa Ma’aikatar Kudi.

Haka kuma, Bashir Tanimu Gambo, wanda tsohon kwamishinan kuɗi ne, an tura shi zuwa Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi da Sarautu.

Sauran sauye-sauyen, sun haɗa da tura Alhaji Yusuf Rabi’u Jirdede daga Ma’aikatar Ayyuka na Musamman zuwa Ma’aikatar Kasuwanci, Ciniki da Zuba Jari.

A ɗaya ɓangaren, Alhaji Adnan Nahabu, wanda a baya yake jagorantar Ma’aikatar Kasuwanci, Ciniki da Zuba Jari, yanzu shi ne Kwamishinan Ayyuka na Musamman.