Radin suna ya ja wa mai kare daurin kwana 10 a gidan yari
Yan sanda a gabashin kasar China sun tsare wani matashi mai suna Ban dan shekara 30 mai kiwon karnukan Turawa na tsawan kwanaki 10 saboda laifin rada wa karnukansa biyu suna. Sunan da ya rada wa karnukan da harshen Sinanci na nufin Gwamnatin China, na biyun kuma na nufin Ma’aikatan Gwamnati. A ranar Litinin da […]
Yan sanda a gabashin kasar China sun tsare wani matashi mai suna Ban dan shekara 30 mai kiwon karnukan Turawa na tsawan kwanaki 10 saboda laifin rada wa karnukansa biyu suna.
Sunan da ya rada wa karnukan da harshen Sinanci na nufin Gwamnatin China, na biyun kuma na nufin Ma’aikatan Gwamnati.
A ranar Litinin da ta gabata ce ‘yan sanda suka kai wa Ban, sammaci bayan wallafa sunan karnukan a shafin sada zumunta ‘WeChat’ na kasar China, saboda ya radawa karnukansa suna ‘Chengguan da Dieguan’. Manufar sunan farko shi ne, jami’an gwamnati masu magance kananan laifuka yayin da suna na biyu ke nufin ma’aikatan unguwanni, kamar masu kula da ababen hawa. Ban, ya ce bai san rada wannan sunan karnukan ya saba dokar kasar ba, shi kuma ya yi ne a matsayin barkwanci, amma sai jami’an ‘yan sanda ba su fahimci hakan ba, suka fara bincike har zuwa lokacin aka yi ta yada sunan karnukan a shafukan sada zumunta na zamani.
Wani jami’in dan sanda ya bayyanawa kafar sadarwa ta Beijing News cewa, wannan sunan karnukan da Ban, ya rada ya fusata wasu jama’a da dama a shafukan sada zumunta kuma hakan na alakanta garin da rashin samun ci gaba, hakan zai iya kawo nakasu a fannin ci gaban kasar da mahukunta biranen kasar ta yadda za su fassarar sunayen da aka radawa karnukan”.
Ban ya bayyana cewa, “Ba ni da masaniya game da wannan dokar, ban san hakan ya sabawa dokar kasa ba”. Amma wannan wani ra’ayi ne, hakan yasa akan tsare Ban a gidan yari kwana 10 a birnin Diangyang, saboda laifin yada bayanan cin mutunci da kuma taka dokar mahukunta.
Tsarewar ‘yan sanda da suka yi wa Ban ya janyo muhawara a shafukan sadarwa na zamani, wasu dai na mayar da martani akan cewa, sai da matashin ya nemi izini kafin ya rada sunan karnukan, mafi yawan masu bibiyan shafin da aka wallafa wannan rahoton sun bayyana fushinsu game da hukuncin da aka yankewa Matashin.
Wani mai bin shafin tambaya ya yi kamar haka: “A fada mini wace doka ce ta ce, kar a rada wa kare sunan Chengguan?”