Rafael Benitez ya zama sabon kocin Everton
Tsohon kocin na Liverpool ya kulla yarjejeniyar kaka uku da Everton.
Rafael benitez
Kungiyar kwallon kafa ta Everton da ke buga gasar Firimiyar Ingila, ta dauki Rafael Benitez a matsayin sabon kocinta wanda zai ja ragamar horas da ’yan wasanta a kaka mai zuwa.
Benitez mai shekaru 61 wanda kuma tsohon kocin Liverpool ne ya kulla yarjejeniyar kaka uku da Everton.
- JAMB ta yi martani kan sake gudanar da jarrabawar UTME a bana
- Ya kamata farashin man fetur ya haura N280 —NNPC
Sabon kocin na kasar Sifaniya ya maye gurbin Carlo Ancelotti wanda ya ajiye aiki tun a farkon watan Yuni ya koma Real Madrid, inda shi ma a can ya maye gurbin Zinedine Zidane.
Kungiyar karshe da Benitez ya horar a Firimiyar Ingila ita ce Newcastle United, wadda ya ajiye aikin a Yunin 2019.
Daga nan ne kuma ya koma horar da kungiyar Dalian Professional FC a China kuma suka raba gari a watan Janairu bayan shafe watanni 18 tare.
Everton ta ce Benitez zai soma aikin horar da yan wasanta yayin da za su dawo wasannin sharar fage a ranar 5 ga watan Yuli.