Rage albashi da gwamnoni ke yi alamu ne na gyara amma – Shehu Sani
dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce rage albashi da wasu gwamnonin kasar nan suka yi alamu ne na son a yi gyara da kuma kawo canji, sai dai y ace ba a nan take ba, domin albashin Gwamna ko ’yan majalisa kadan ne a kan dimbin kudin da […]
dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce rage albashi da wasu gwamnonin kasar nan suka yi alamu ne na son a yi gyara da kuma kawo canji, sai dai y ace ba a nan take ba, domin albashin Gwamna ko ’yan majalisa kadan ne a kan dimbin kudin da ake samu a jihohi da tarayya.
Sanata Shehu Sani ya ce idan ana son gaskiya wajibi ne a rika fada wa jama’a sauran kudaden da ake kashewa wajen kwangila da wadanda ake bai wa ma’aikatu da kuma nawa aka samu daga asusun tarayya.
Sanata Sani ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya jim kadan bayan ya kai ziyara ofishin wakilan kafofin watsa a Kaduna.
Ya ce sauran bangarorin da ya wajaba a rika yi wa jama’a bayani a kai sun hada da kudin da ake kashewa kan harkar tsaro da na gidaje da ilimi da lafiya da ake narka biliyoyin Naira, kuma tana nan ake satar dukiyar jama’a, ba ta bangaren albashin Gwamna ko ’yan majalisa ba.
Sanata Sani ya ce albashin da ake biyan ’yan majalisa a kasar nan ma ya yi yawa idan aka yi la’akari da halin rashin kudi da talakawa ke ciki “Kuma bai kamata a ce wasu ’yan Najeriya suna dibar kudi masu dimbin yawa haka ba, alhali talakawa na cikin wahala,” inji shi.
Game da rikicin Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani ya ce an kira talakawa cewa su zabi Jam’iyyar APC sun kuma zabe ta, “Saboda haka bai kamata wasu daga cikinmu da aka zaba a APC su je su hada kai da ’yan PDP domin neman mukami. Wannan canji ba zai tabbata ba idan muka hada kai da mutanen da aka yi barna da su a baya,” inji shi.
Ya ce amma tunda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi aiki da Saraki su ’yan majalisa ba su da ’yancin su ce ba za su yi aiki da shi ba. “Amma babbar matsalarmu ba ma ta Saraki ba ce. Dole ne mu ’yan APC mu hada kai a majalisa domin mu tabbatar da cewa duk wasu kudirori da ake nema a majalisa su samu shiga in ba haka ba kuwa akwai matsala.