Rage farashin mai zuwa Naira 87 ya yi kadan – Alhaji Iliyasu
Wani dan kasuwa da ke zaune a garin Jos babban birnin Jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad ya bayyana cewa rage farashin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi dag a Naira 97 zuwa 87 a karshen makon da ya gabata, ya yi kadan. dan kasuwar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da […]
Wani dan kasuwa da ke zaune a garin Jos babban birnin Jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad ya bayyana cewa rage farashin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi dag a Naira 97 zuwa 87 a karshen makon da ya gabata, ya yi kadan.
dan kasuwar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya. Inda ya ce: “Domin duk wanda ya san halin da kasuwar mai take ciki a kasuwar duniya a yanzu, idan ya ji wannan abu da gwamnatin kasar nan ta yi na rage kudin man fetur a Najeriya zai ce wannan rage farashin mai bai yi ba. Yakamata tun kafin wannan lokaci a ce gwamnatin Najeriya ta rage kudin mai zuwa Naira 50 ko 60,” inji shi.
Ya ce a yanzu farashin gangar mai ya karye a kasuwannin duniya, “domin haka ayyukan raya kasa da gwamnati take yi sun tsaya, ba a biyan ma’aikata albashi a wasu jihohi, domin an kasa bai wa gwamnatocin jihohi kudin da suka kamata. Don haka ya kamata a saukar da farashin man ta yadda talakawa za su amfana,” inji shi.