Rage farashin simintin Dangote ya zama dodorido

Ga alama rage farashin simintin da kamfanin dangote ya yi daga Naira 1,700 zuwa 1,000 a makon jiya ya zama dodorido, inda ’yan kasuwa masu sayar da siminti suka ce ba su gani a kasa ba, wadansu sun soki sabon farashin, wasu kuma suka yaba wa kamfanin. Wani mai sayar da siminti a yankin Agege […]

Rage farashin simintin Dangote ya zama dodorido
Rage farashin simintin Dangote ya zama dodorido

Ga alama rage farashin simintin da kamfanin dangote ya yi daga Naira 1,700 zuwa 1,000 a makon jiya ya zama dodorido, inda ’yan kasuwa masu sayar da siminti suka ce ba su gani a kasa ba, wadansu sun soki sabon farashin, wasu kuma suka yaba wa kamfanin.

Wani mai sayar da siminti a yankin Agege mai suna Funsho Fulorin ya shaida wa Aminiya ta wayar salula a ranar Litinin cewa bai ji dadin rage farashin ba.
Ya ce “Gaskiya ban ji dadin yadda kamfanin ya rage farashin ba, saboda simintin da muka saya a kan farashin baya yaya za mu yi da shi? Ka ga dole ka fadi. Misali ka sayi siminti fiye da Naira 1,500 idan ka sayar da shi 1,000 ka fadi. Ka ga kamata ya yi kamfanin ya bari idan mun sayar gaba daya sai ya rage farashin. Ina mai tabbatar maka masu sayar da siminti da yawa za su karye.”
Ya ce ba masu sayar da siminti ba kawai kamfanonin siminti da dama za su yi asara mai yawan gaske, “ba a ma maganar kananan ’yan kasuwa, su karshensu ya zo ke nan.” Inji shi.
Mista Jaku Harrison wani mai sayar da siminti a kan titin Egbeda ya bayyana rashin jin dadinsa sakamakon rage farashin. “Ban ji dadi ba saboda duk simintin da na saya ya zama asara ke nan. Kuma tun daga ranar da kamfanin dangote ya rage farashin zuwa Naira 1,000 mutane suka daina sayan simintinmu a kan farashin da. Da mutum ya zo sai ya ce ba zai saya a kan farashin da ba tun da dangote ya rage farashin simintinsa.”
Sai dai Mista Tunde Farook ya yaba wa matakin da kamfanin ya dauka na rage farashin. “Mun ji dadi sosai. Yanzu za mu sayi siminiti a kan farashi mai sauki ba kamar da ba, da ’yan kasuwa suke tsauwala mana ba. Ga dukkan alama mutane da yawa za su mallaki gidajen kansu ba tare da wata matsala ba.” Inji shi.
Alhaji Abdullahi Bako mai sayar da siminti a Titin Ibrahim Taiwo da ke birnin Kano, ya ce a yanzu suna sayar simintin ne a kan Naira 1,408 a maimakon Naira 1,785 da yake a da, wato an samu ragin Naira 377 ke nan.
Ya ce “Da farko an fada mana simintin filasta za a yi daban, wanda shi ne za a sayar a kan Naira 1,000. Yanzu sabon farashin ya hada mu jayayya da masu saye, inda a kowane lokaci suka zo sai su ce an mayar da farashi Naira 1,000. A yanzu ba ma samun masu sayen simintin kamar da. A Kano simintin dangote ya fi na sauran araha, inda ake sayar da na Ashaka Naira 1,810, na Sakkwato Naira 1,980, na Bua a kan Naira 1,700.”
Jamilu Muhammad dillalin siminti a kasuwar sumunti da ke daf da tashar jirgin kasa ta Kano ya ce, a sakamakon sanar da ragin farashin, an jawo wa ’yan kasuwar da suka sara a kan tsohon farashin asara.
Ya ce kasuwar siminti ta cushe, domin ya cika kasuwa, sannan cinikinsa ya tsaya.
Alhaji Ibrahim Bosso dillalan simintin dangote a Jihar Neja ya bayyana jin dadinsa game da kokarin da kamfanin dangote ke yi na samar wa jama’a siminti a farashi mai rahusa, ta yadda kowane magidanci zai mallaki muhalli cikin sauki.
“Matsalar da aka samu ita ce kamfanin bai zauna da mu kafin ya yanke hukuncin rage farashin ba, wanda hakan zai jawo wa ’yan kasuwa asara. Yanzu sun hada mu fada ne da jama’a.” Inji shi
Malam Yahaya Ashiru dillali siminti a PZ Sabongari a Zariya ya ce farashin siminti yana nan yadda yake a Zariya.
Ya ce “Nima haka na ji a bakin mutane cewar farashin siminti ya sauko zuwa Naira 1,000. Idan haka ne wannan labari ne na farin ciki, amma na ji kamar almara domin sama da shekara goma farashin siminti na sama da Naira 1,000, ka ga ko idan aka ce ya sauko, za a samu sauki. Wanda nake sayarwa har yanzu farashinsa Naira 1,700 ne, kuma haka mutane suke saya. A nan Zariya ban ji wani wuri da ake sayar da simintin dangote kasa da farashin da nake sayarwa ba.”
Malam Muhammad Sani mai sayar da siminti a bakin kasuwar Tudun Wada, Zariya cewa ya yi “Ni ma haka na ji labarin nan jiya (Talata), amma ban samu sako daga kamfanin dangote a rubuce ko ta waya ba, wadanda kake gani yanzu za a loda a mota a kan farashin Naira 1,700 ne.”
Malam Isa ya ce ya sayi buhu 50, kuma kowane buhu daya da ya saya a kan Naira 1,700, za su yi farin ciki idan rage farashin ya tabbata.
Paul Mathew dillalin siminti da ke Lafiya a Jihar Nasarawa har yanzu ba a fara sayar da siminti a kan sabon farashi ba, zai fara sayar da siminti a kan sabon farashi ne idan aka kawo masa wani siminti a kan farashin da idan ya sayar Naira 1,000 zai samu riba, don ya fi so farashin ya sauka.
Musa Lawal mai siminti a Tudun-Gwandara, a Lafiya ya ce kamfanin dangote bai bayyana ainahin lokacin da za a fara sayar da simintin a kan sabon farashin ba.
“Da kamfanin ya ce a farkon wata mai zuwa ne, yanzu kuma ya ce a tsakiyar wata mai zuwa, har yanzu ana kawo mini siminti kan farashin da na saba saya.” Inji shi.
Sai dai a wata sanarwa da Kamfanin dangote ya fitar a makon jiya ta hannun Manajan Daraktan rukunin simintin dangote mai suna Mista Debakumar Edwin, ya ce, kamfanin ya rage farashin ne don taimakon kasa, musamman bukatar da ake da ita a bangaren gine-gine don rage kimanin miliyan 20 na kudin gidaje a kasar nan.