Rage kashe kudin sharholiya ya yi daidai – Yusha’u Aliyu
Wani masanin tattalin arziki, Malam Yusha’u Aliyu ya bayyana goyon baya kan daukar matakan rage kashe kudi na gwamnati, sai dai ya soki amfani da kalma mai tsauri na “tsuke bakin aljihu” da Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da shi a yayin bayyana shirin. Malam Yusha’u Aliyu ya ce, amfani da Kalmar tsuke baki aljihu […]
Wani masanin tattalin arziki, Malam Yusha’u Aliyu ya bayyana goyon baya kan daukar matakan rage kashe kudi na gwamnati, sai dai ya soki amfani da kalma mai tsauri na “tsuke bakin aljihu” da Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da shi a yayin bayyana shirin.
Malam Yusha’u Aliyu ya ce, amfani da Kalmar tsuke baki aljihu na iya tsoratar da jama’a tare da jawo rudani. “Ban ga laifin dakatar da daukan nauyin zuwa tarurrukan shan shayi ba, ko tsawwala haraji a kan shigo da giya mai tsada da manyan mutane ke nuna kasaita wajen shan ta da sauran abubuwan kashe kudi na sharholiya da gwamnati ko masu dukiya ke yi ba,” inji shi.
Ya ce koda ya ke faduwar farashin mai da ya sa gwamnati daukan matakin na da dalilai iri-riri da suka hada da karan-tsaye da kasashe irin su Saudiyya ke yi na kara adadin man da suke kaiwa kasuwannin duniya fiye da adadin da kungiyar OPEC ta amince, don biyan bukatar Amurka, ya ce karuwar kasashe masu hako mai da suka hada da Sudan ta Kudu da Angola da Jamhuriyar Nijar a nan Afirka ya taimaka wajen faduwar man.
Malam Yusha’u ya ce wani dalilin kuma shi ne kasashen duniya na dada nemo hanyar rage bukatar mai, saboda dalilai daban-daban, ciki har da bayyanar wani sinadari mai suna shel petroleum da a ke yin manfani da shi wajen yin man fetur, sai kuma karfin da Dalar Amurka ta kara yi, wanda hakan ke cutar da kudaden sauran kasashe.
Masanin tattalin arzikin ya ce dogaro dungurugum da Najeriya ta yi a kan man fetur tare da watsi da sauran hanyoyin samar da kudin shiga, na iya girgiza arzikinta a duk lokacin da irin haka ya kasance. “Sai kuma gibi da ake samu a kasafin kudin kasa duk shekara sakamakon rashin aiwatar da kasafin yadda aka tsara shi,” inji shi. Ya ce duk da cewa farashin mai ya yi ta tashi daga Dala 17 a lokacin da Najeriya ta dawo mulkin dimokoradiyya a 1999, har wani lokaci da ya kai Dala 150, ya ce ta gaza cin gajiyar kudin ta hanyar zuba jari a wasu fannoni masu ma’ana.
Ya ce mafita ita ce Najeriya ta rungumi wasu hanyoyin samun kudin shiga na daban, sannan ta rika bin tsarin kasafin kudi yadda a ka tsara, tare da samar da ayyukan yi ga jama’ar kasa.