Rage kuɗin simintin BUA ya jawo ruɗani
Dillalai sun ce ba zai yiwu a sayar da buhun siminti a farashin da Kamfanin BUA ya ambata ba.
A farkon wannan mako ne Kamfanin Siminti na BUA, ya sanar da cewa daga ranar Litinin 2 ga watan Oktoba farashin buhun simintinsa zai koma Naira 3,500.
Kamfanin ya ce ya rage farashin ne sakamakon saukin da ya samu wajen sayen kayayyakin da ake sarrafa siminitin da kuma kammala wasu manyan ayyukan kamfanin da a baya suke haifar da tsadar simintin.
- Shugaba Alassane Ouattara ya rusa gwamnatin Ivory Coast
- FIFA ta bayyana kasashen da za su shirya gasar cin kofin duniya ta 2030
A cewar kamfanin, wannan wani mataki ne na ganin ’yan Nijeriya sun samu damar yin gine-gine cikin sauki da kuma saukaka farashin kayan gineginen.
Kamfanin ya ce da zarar an kammala aikin sababbin layukan da kamfanin ke yi a yanzu, zuwa sabuwar shekara, kamfanin zai sake duba yiwuwar rage farashin.
A cewar sanarwar: “Dangane da bayanin da muka fitar a baya na niyyar da muke da ita ta rage farashin siminti da zarar mun kammala bude sababbin layukanmu a karshen shekara, domin bunkasa kayan gini da sashin gine-gine.
“A yunkurinmu na rage farashin kayayyakinmu da sake nazartar ayyukanmu lokaci zuwa lokaci, Hukumar Gudanarwar Kamfanin BUA na sanar da abokan huldarta da masu ruwa-da-tsaki da sauran al’umma cewa daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023, mun cim ma matsayar rage farashin simintin.
“A kan haka, daga yanzu za a sayar da buhun simintin BUA ne a kan Naira 3,500 domin ’yan Najeriya su fara cin moriyar farashin kafin mu kammala tsare-tsarenmu.”
Kamfanin ya shawarci dillalansa su tabbatar jama’a sun amfana da wannan sabon farashi kuma kamfanin zai sanya ido wajen ganin ana bin umarnin amfani da sabon farashin ba tare da wata tangarda ba.
In za a tuna a makonnin da suka gabata ne bayan wata ziyara da ya kai wa Shugaban Kasa Bola Tinubu, Shugaban Rukunin Kamfanin BUA, Alhaji Abdul-Samad Isyaka Rabi’u, ya sanar da cewa, kamfanin ya shirya tsaf domin rage farashin siminti a Najeriya zuwa Naira 3,500 ko kasa da haka.
Sai dai lamarin ya jawo rudani, inda wasu suke cewa sanarwar ba ta yi gamsasshe bayani ba a kan nawa ake sayar da siminitin a kamfanin a baya, wanda hakan ya sa mutane suke tambayar nawa farashin zai zama a kasuwa bayan an biya kudin kai shi kasuwa, kasancewa a kasuwa mutane suke saya ba a kamfanin ba.
Haka kuma, wasu suna cewa abinci ya kamata a rage kudinsu ba simintin ba, suna masu cewa masu kudi ne suke iya yin gini.
Aminiya ta lura da yadda wasu suke caccakar Dangote, inda suke cewa shi ma ya kamata ya rage farashin nasa simintin.
A ziyarar da Aminiya ta kai ga dillalan siminti a kasuwanni sun ce wannan ragi da Kamfain BUA ya yi almara ce kawai.
Alhaji Jamilu Aliyu wani dan kasuwar sayar da siminti a Kamfanin BUA ya ce, “Ai wannan bayani na Kamfanin BUA akwai lauje cikin nadi domin kuwa a bayanin da mka ji na nuna cewa, duk wanda zai je can wajensu wato kamfanin ya saya tilas shi zai biya motar da za ta kawo masa simintin zuwa garinsa.
“Misali idan mutum yana cikin garin Damaturu kowane buhun siminti sai ya biya masa sama da Naira 1,000 kudin mota saboda kudin man dizel ya wuce Naira 1,000 a kowace lita.
“A karshe idan ka sayo simintin a kan Naira 3,500 to akwai yiwuwar zai zo maka Damaturu a sama da Naira 4,650 tunda ai bayan kudin mota za kuma ka biya kudin dauka da saukewa, to ina saukin yake?”
Dan kasuwar ya kara da cewa, “Idan misali su manyan dillalanmu za a kawo musu kowane buhu a kan Naira 3,500, to ai akwai kudin dauka da saukewa, mu kuma masu sayarwa dole za mu biya kudin motar da za ta kai mana shagunanmu da garuruwanmu, a karshe kowane buhu kan iya tashi a kusan Naira 4,700.
“Mu kuma dole mu dan ci riba to ka ga kafin komai ya yiwu kowane buhu zai iya kaiwa Naira 5,000 kamar yadda yake a yanzu.
“Don haka a ganina lokaci ne zai nuna yaya lamarin zai kasance na yiwuwar saukar farashin simintin kamar yadda aka ambata,” in ji shi.
Alhaji Adamu Maisiminti da ke Jihar Yobe cewa ya yi, “A gaskiya a shirye muke mu saukar da farashinsa matukar mun same shi da sauki kamar yadda kamfanin ya ambata.
“To amma a yanzu haka muna da tsohon kaya da muka saya a tsohon farashi. Ke nan koda a ce an saukaka farashin to ka ga dole sai mun sayar da tsohon siminitin a tsohon farashinsa na Naira 5,000 kafin a sayar da sabon in har an kawo mana shi kamar yadda kamfanin ya ambata.”
“Fatanmu shi ne, Allah Ya sa wannan alkawari da Kamfanin BUA ya yi ya tabbata.
“Su ma sauran manyan kamfanonin yin siminti da ke kasar nan irin su Ashaka, Dangote da sauransu, su bi sahun Kamfanin BUA ko al’umma sa samu sa’ida,” in ji shi.
A Jihar Kano, binciken Aminiya ya gano cewa dillalan siminti sun nuna rashin jin dadinsu game da batun rage farashin da kamfanin ya yi domin ya janyo musu rashin ciniki.
Alhaji Hassan Ibrahim Giwa, babban dillalin siminti ne a Jihar Kano ya ce farashin simintin zai iya zuwa gare su a kan Naira 4,600, don haka idan sun tashi sayarwa za su sayar da shi a kan Naira 4,800.
“Ya kamata jama’a su fahimci cewa wannan farashi na Naira 3,500 farashin kamfanin ne. Idan muka je saye za mu biya kudin mota inda akalla zai zo mana Kano a Naira 4,600. Sannan mu dan dora ribarmu a kai.
“To batun mutane su yi tunanin za a sayar musu a kan Naira 3,500 ba abu ne mai yiwuwa ba,” in ji shi.
A cewarsa sabon farashin bai bambanta da na baya ba domin ko a da suna sayar da buhun simintin a kan Naira 4,800.
Ya ce duk da cewa a wannan lokaci suna fama da jama’a bisa turjiya a kan farashin amma ya san zuwa wani lokaci jama’a za su fahimci gaskiyar lamarin.
“A yanzu zan iya cewa ciniki ya tsaya cak saboda idan jama’a sun zo sai su ce ai farashin ya ragu.
“Duk bayanin da za mu yi musu mun yi, amma sun gaza ganewa. Sai dai na san zuwa wani lokaci gaskiya za ta yi halinta, mutane za su san gaskiyar alamari,” in ji shi.
Shi ma wani dillalin siminti a Kano, Alhaji Hassan ya ce babu abin da rage farashin siminti da Kamfanin BUA ya yi, illa hada su fada da mutane.
“Wannan sanarwa da Kamfanin BUA ya yi hada mu fada da mutane ta yi, domin kowa ya zo sayen kaya sai ya nuna cewa ai farashin ya sauko.
“Don haka wallahi harkokinmu sun tsaya, ko bulo da muke yi mutane suna tunanin su ga canjin farashin nan take, wanda hakan ba zai yiwu ba.
“Sun manta cewa kayanmu da ke kasa mun saye su ne a tsohon farashin,” in ji shi.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Kamfanin Dangote game da rashin rage farashin da bai yi ba abin ya ci tura, inda jami’an kamfanin suka ce a nemi babban ofishinsu da ke Abuja ko Legas don karin bayani.