Rage kudin wutar lantarki

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bakin Hukumar Lura da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da rage kashi 50 cikin 100 na kudin wutar lantarki. Shugaban hukumar Mista Sam Amadi ya bayyana wannan sabon tsarin zai fara aiki a karshen wannan watan, sun kuma yanke wannan hukuncin ne bayan sun cire kudin […]

Rage kudin wutar lantarki
Rage kudin wutar lantarki

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bakin Hukumar Lura da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da rage kashi 50 cikin 100 na kudin wutar lantarki. Shugaban hukumar Mista Sam Amadi ya bayyana wannan sabon tsarin zai fara aiki a karshen wannan watan, sun kuma yanke wannan hukuncin ne bayan sun cire kudin da kwastomomi za su rika biya wanda aka kira ‘collection losses’.

Mista Amadi ya ce sun rage kudin wutar ne bayan wasiku da korafe-korafen da jama’a suka aike wa hukumarsu, inda suka bukaci a rage kudin wutar.
Ya jaddada masu masana’antu da ’yan kasuwa a karkashin kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya sun yi korafin sakamakon karin kudin wutar lantarki, a yanzu kudin da suke kashewa wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum ya karu, wanda hakan zai tilasta musu su rage yawan ma’aikata, inda a karshe suka bukaci hukumar ta rage kudin wuta.
Amadi ya ce dalilin wadannan koraffe-korafen Hukumar NERC ta shirya taron jin koke-koken jama’a a bangarori daban-daban, sannan ta gana da shugabannin gudanarwar kamfanonin da suke rarraba wutar lantarki kafin su yanke hukuncin rage kudin wutar.
Tabbas duk abin da ya shafi rage kudin kayayyaki abu ne na farin ciki a wurin kwastomomi a kasar nan, dalilin halin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki, sai dai matakin rage kudin wutar bai sanya kwastomomi farin ciki ba, saboda mene ne amfani rage kudin bayan ba a samun wuta a kasar nan?
A kasar nan da yawancin wurare suke fama da karancin wutar lantarki fiye da watanni, sanar da rage kudin wutar ya sanya mutane yi wa batun habaici. kididdiga ta tabbatar da kashi 40 cikin 100 na ’yan kasar nan ne suke amfani da wutar lantarki, inda hakan ya nuna fiye da mutum miliyan 90 ba sa samun damar amfani da wutar lantarki.
Halin da ake ciki dangane da matsalar wutar lantarki a kasar nan ba kadan ba ce, duk da kashe biliyoyin Dala don inganta harkar wutar lantarki a kasar nan. Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa ’yan Najeriya alkawarin samar musu wutar lantarki ta tsawon awa 18 a kowace rana, wannan alkawari ba a cika shi ba, tun da aka yi wannan alkawarin ma al’amarin wutar lantarki kara tabarbarewa ya yi.
A kullum sai gwamnati ta fito da wani dalili da take dogara da shi a matsayin dalilin da ya haifar da rashin isasshiyar wutar lantarki a kasar nan. Abin dubawa a nan shi ne, ba a samar da duk wadansu matakan samar da isasshiyar wuta a kasar nan ba, don haka rage kudin wutar ba shi da ma’ana, sai dai a yi amfani da hakan wajen kamfen din siyasa. daya daga cikin matakan da za a bi wajen inganta wutar lantarki shi ne, a karfafa batun tsarin amfani da wuta ta hanyar mita.
Yawancin masu amfani da wuta ba su mita duk da cewa suna biyan makudan kudi wajen sayan wadannan mitoci. Rashin amfani da wadannan mitoci ya sanya ba za a gane yanayin yadda ya kamata a biya kudin wuta ba.
A yanzu halin da ake ciki za a iya fadawa cikin rikici saboda ba za a rika samun wuta a tsawon watanni ba, amma za a rika kawowa bil din kudin wuta na wadannan watannin.
An kara kudin wuta ne saboda kamfanonin da suke rarraba wuta sun yi korafin cewa ba za a samu isasshiyar wuta a kan farashin da kwastomomi suke biya a da ba, wannan korafin ya sanya Hukumar NERC ta sanar da karin kudin wuta daga Naira 1 zuwa Naira 5 a kan kilowatt a awa, duk da cewa akwai bambanci idan wurin da ake amfani da wutar gida ne ko kuma kamfani ko wurin da ake gudanar da kasuwanci.
Idan ba a manta ba a watan Mayun bara Hukumar NERC ta sanar da cewa sabon tsarin biyan kudin wuta zai fara amfani daga ranar 1 ga watan Yuni, sannan duk kamfanonin da ke rarraba wutar za su rika cajin Naira 750 bisa tsarin MYTO.
Batun gaskiya shi ne ba a gane manufar gwamnati dangane da cewa sabon tsarin zai fara amfani ne bayan an kammala zaben shugaban kasa ba.
Ba tun yau ake samun labarai da alkawuran cewa za a inganta wutar lantarki ba, don haka dalilin da jama’a ba su dauki batun da muhimmanci ba, dalilin da ya sa ke nan ko da aka bayyana kara karfin wutar lantarki da megawatt 110 daga kamfanin tama da kara da samar da wutar lantarki na Ajakuta da ke Jihar Kogi mutane ba su kasance cikin murna ba.
Gaskiya magana ita ce idan aka samu wadatacciyar wutar lantarki tattalin arziki zai bunkasa, inda hakan ba zai sa kwastomomi su ki biyan kudin wuta ba.