Rage yawan masu tabin hankali
Kwanan nan ne Babbar Daraktar Asibitin Mahaukata na Tarayya da ke garin Yaba a Jihar Legas, Dokta Oluwayemi Ogun ta nuna rashin jin dadinta bisa yadda ake samun karuwar masu tabin hankali a cikin matasan kasar nan. Ta ce matashi 1 daga cikin matasa 5 na da matsalar tabuwar hankali, sannan 1 cikin 4 na […]
Kwanan nan ne Babbar Daraktar Asibitin Mahaukata na Tarayya da ke garin Yaba a Jihar Legas, Dokta Oluwayemi Ogun ta nuna rashin jin dadinta bisa yadda ake samun karuwar masu tabin hankali a cikin matasan kasar nan. Ta ce matashi 1 daga cikin matasa 5 na da matsalar tabuwar hankali, sannan 1 cikin 4 na manya suna samun matsalar koda sau daya ne a rayuwarsu. Dokta Ogun ta yi wannan bayani ne a wani taron kara wa juna sani a makon jiya da aka shirya domin tunawa da Ranar Masu Tabin Hankali ta Duniya mai taken ‘Matasa da matsalar tabin hankali a wajen canja yanayin duniya.’
Ta ce matasa masu shekaru tsakanin 14 zuwa 35 suna fama ne da matsalar yawan tunani da damuwa, inda ta ce yawancin matasan da suke fama da damuwa ba su cika damuwa da zuwa asibiti ba. A cewarta kashi 75 cikin 100 na tabin hankali na farawa ne kafin matashi ya kai shekara 18, sannan rabin manya masu tabin hankali ciki har da masu ciwon mantuwa suna farawa ne kafin shekara 14. Ta kara da cewa yawancin mutane ba sa zuwa asibiti sai abin ya fi karfinsu. Sannan ta kara da cewa yawancin mutane masu tabin hankali ana ware su ne ko kuma suna tunanin ba za su iya samun waraka ba, don haka sai su ta’allaka da shawarwarin da suke samu daga ’yan uwa da abokan arziki, wanda kuma wani lokacin suke bayar da shawara mara kyau.
Haka a jawabinsa ga manema labarai a garin Abeokuta a ranar Masu Tabin Hankali ta Duniya, Babban Likitan Asibitin Mahaukata na Aro da ke Abeokuta, Dokta Timothy Adewale ya nuna shan miyagun kwayoyi a matsayin abin da ke kan gaba wajen jawo matsalar tabuwar hankali, inda ya ce hakan na jawo zinace-zinace da tukin ganganci da sauransu. Adewale ya kara da cewa damuwa ce abu na uku da ke jawo matsalar tabuwar hankali a tsakanin matasa. Damuwa na da fadi sosai, wadda ta hada da dadewa cikin yanayi mara kyau da kuma rashin dagewa wajen ci gaba da al’amuran yau da kullum.
Tabuwar hankali ciwo ne na rashin cikakkiyar lafiyar kwakwalwa wadda dadewa cikin yanayi mara kyau da rashin shiga cikin al’amuran yau da kullum ke iya jawowa, wanda ke jawo matsala a rayuwa. Abubuwan da ke jawo matsalar suna da yawa, akwai manya akwai kanana wadanda ke da alaka da yanayin ciwo da kuma mai ciwon. Matsalar jiki da tunani da yanayin wajen zama duk suna iya kawo matsalar ba sai guda daya ba kawai.
Yadda yanayin wajen zama ke jawo matsalar tabuwar hankali sun hada da abubuwan da mutum ke mu’amala da su da matsalar gida da rashin mu’amala mai kyau da mutane da shan miyagun kwayoyi da kuma damuwar matsalolin rayuwa da talauci da bashi da tashin hankali da ya auku saboda hadari da rikici da warewa daga cikin mutane da nuna bambanci da mutuwar masoyi da rabuwar aure da rashin wajen zama da faduwa jarrabawa da rashin aikin yi da kora daga aiki.
Daga cikin alamomin tabuwar hankali akwai canjin yanayi da tunani marar amfani da yawan jiji-da-kai da wasu ayyuka na daban. A cewar wani ma’aikacin lafiya, matsalar tabuwar hankali ba ta cika nunawa a fili ba, amma damuwa na iya jawo rama da gajiya. Ware kai daga mutane da yawan fushi da tunanin rashin taimako daga mutane suna cikin kananan abubuwan da ciwon ke jawowa, amma kuma idan abin ya yi tsanani, yana iya sa wa mutum ya kashe kansa.
Domin rage yawan masu tabuwar hankali a cikin ’yan Najeriya musamman matasa, ya kamata gwamnati ta lura da lafiyar ’yan kasa, ta hanyar dagewa da wayar da kan mutane a kan amfanin zuwa asibiti lokaci bayan lokaci duk lokacin da suka ji wata matsala na damunsu. Ya kamata kuma gwamnti ta bude cibiyoyin wayar da kan mutane a duk asibitocin gwamnati har da wadanda suke cikin karkara.
Gwamnatoci a matakin jiha da kananan hukomomi ya kamata su habbaka ayyukan ofisoshin kula da jin dadin mutane kamar yadda suke a da. Jami’in kula da jin dadin mutane zai iya taimakawa wajen samar wa mutane masu tabuwar hankali zuwa asibiti da samun magani. Sannan idan gwamnati ta yi aiki mai kyau, zai taimaka matuka wajen rage yadda yanayin wajen zama ke jefa mutane cikin matsalar tabuwar hankali.