Ragin farashin fetur: sauki ko tsada?
A tsakar daren Lahadi 18 ga wannan watan Ministar Albarkatun man fetur Misis Dieziani Alison-Madueke, ta fada wa wani taron manema labarai a Abuja cewa daga wannan lokacin, gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur da N10, akan kowace lita, daga N97, yanzu ya koma N87, farashin da ta ce ya fara aiki nan take. […]
A tsakar daren Lahadi 18 ga wannan watan Ministar Albarkatun man fetur Misis Dieziani Alison-Madueke, ta fada wa wani taron manema labarai a Abuja cewa daga wannan lokacin, gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur da N10, akan kowace lita, daga N97, yanzu ya koma N87, farashin da ta ce ya fara aiki nan take. Ta fadi cewa tuni gwamnatin tarayya ta umurci Hukumominta, wato Hukumar daidaita farashin man fetur da dangoginsa, wato PPPRA, da ta Fannin kula da albarkatun man fetur, wato DPR , da lallai su tabbatar da cewa sabon farashin ya kama aiki nan take a dukkan fadin kasa. Ragin da Ministar ta ce ya samu ne daga irin yadda farashin danyen man fetur yake ta faduwa a kasuwar duniya a `yan watannin nan, inda ta yi fatan `yan kasa za su amfana da wannan ragi yadda ya kamata.
Dama tun daga watan Nuwamban bara da farashin danyen man fetur ya fara faduwa a kasuwar duniya, ba kakkautawa, daga Dalar Amurka $110, akan kowace ganga, har ya gangaro yanzu yana kasa da $50, `yan kungiyoyin kwadago da na kare hakkin bil adama da masana tattalin arzikin kasa da sauran `yan kasa suke ta kiraye-kirayen lallai sai gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur din. kasar nan dai tana cikin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya, wato OPEC, inda ta kan hako sama da gangar danyen mai sama da miliyan biyu, a kowace rana, kuma duk da tana da matatun man fetur hudu, amma tana shigo da kashi 80, cikin 100, na man fetur din da take bukata, wanda aka kiyasta ya kai lita miliyan 40, a kowace rana, baya ga sauran dangoginsa, irinsu man gas da na kanazir da na amfanin masana`antu da ake kira bulak oyel.
Gaza samar da wadataccen man fetur da dangoginsa da kasar nan take bukata, shi ya sanya a koda yaushe gwamnatin kan ce da `yan kasa tana yi masu ciko akan farashin man fetur din da suke amfani da shi, rangwamen da aka dade ana tababa da sahihancin gaskiyarsa, wanda a cikin kokarin gwamnatin tarayyar na janyr hannunta daga wancan sassauci ya sanya daga lokaci zuwa lokaci ta kan yiwa `yan kasa karin farashin man fetur din.
Tarihin karin farashin man fetur a kasar nan ya tabbatar da cewa tun daga shekarar 1973, lokacin Janar Gowon ya yi karin farashin litar mai fetur daga 6k zuwa kwabo 8.45, Janar Murtala ma ya yi nasa a shekarar 1976, daga kwabo 8.45, zuwa kwabo 9k akan kowace lita. Janar Obasanjo shi ya kara farashin man daga kwabo 9k, zuwa kwabo 15.3, wanda ya kai da kashi 70 cikin 100, a tashi daya. Shugaba Alhaji Shehu Shagari, shi ma ya yi karin farashin man fetur din daga kwabo 15.3, zuwa kwabo 20k, a shekarar 1982. Janar Ibrahim Babangida da ya tarar da farashin man akan kwabo 20, ya barshi akan kwabo 70k, bayan ya yi kari har sau biyar a cikin mulkinsa daga shekarun 1986 zuwa 19991. Cif Enest Shonekan da ya gaji Janar Babangida a shekarar 1993, duk da wa`adinsa bai wuce watanni hudu ba, amma sai da ya yi karin farashin man fetur din daga kwabo 70 zuwa N5, karin da ya kai ya nunka sama da sau shidda.
Haka aka yi ta tafiya cikin kwanaki kadan da zuwan Shi ma Janar Sani Abacha da ya zo kan mulki a watan Nuwamban 1993, kafin Allah Ya dauki ransa a ranar 08-06-98, sai da ya yi kari har sau biyar akan N11. Mulkin Janar Abdussalami Abubkar na watanni 11, ya yi karin farashin man sau biyu, inda ya bar farashin man a shekarar 1999, akan N20, kowace lita. Dawowar Janar Obasanjo a zaman shugaban farar hula a jamhuriya ta hudu da muke ciki daga 29 ga watan Mayun 1999, zuwa saukarsa a ranar 29 ga watan Mayun 2007, bayan mulkin shekaru 8, cif, sai da ya yi karin farashin man har sau bakwai, wanda daga N20, da ya tarar da shi, ya tafi ya barshi akan N75, akan kowace lita. Shugaba Umaru Musa `Yar`aduwa da ya gaji Cif Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayun 2007, ya dawo da farashin akan N65, wata daya bayan ya hau karagar mulki, har kuma Allah Ya karbi ransa a watan Mayun 2010, bai kara ko da sisin kwabo ba. Shugaba Dokta Goodluck Jonathan da ya gaji `Yar`aduwa, shi ya kara farashin man fetur din daga N65 zuwa N97, da yake har ya zuwa ranar 18 ga wannan watan da ya sauko da shi daga N97, din zuwa N87.
Babban abin da ya ja wadannan kare-kare na farashin man fetur a kasar nan har ya zuwa wannan lokaci, bayan ka jingina shi da yanayin tattalin arzikin duniya, akwai kuma rashin kulawar mahukuntar kasar nan ta shekaru aru-aru, wajen kin mayar da hankali su rinka tabbatar da akwai wadatattun Matatun man fetur da kuma suke aiki yadda ya kamata, ta yadda za su rinka wadata `yan kasa da dukkan irin man fetur da dangoginsa da suke bukata. Amma kash! sai al`amarin ya zama tamfar an yi mana baki, ta yadda duk gwamnatin da ta zo idan ta shude, sai ka tarar ta fi wadda ta gajeta kulawa da ayyukan Matatun man fetur din, har Allah Ya kawo mu halin da muke ciki da kusan muka dogara kacokan akan shigo da man daga kasashen waje.Wannan ya sa a kullum Mahukuntar kasar ke cewa suna ba da tallafi akan farashin man fetur din. Alhali bayanin da Hukumar lamuni ta Duniya, wato IMF, ta fitar a shekarar 2010, ya tabbatar da cewa kashi 80, cikin 100, na kudin tallafi da Mahukuntar Nahiyar Afirka suke cewa suna kashewa akan man fetur yana zurarewa ne aljihunan masu hannu da shunin nahiyar ne.
Duk da faduwar farashin man fetur din warwas da ake fama da ita a kasuwar duniya, da ragin da aka samu a kasar nan, har yanzu gwamnati wai tana biya mana tallafin N2.84k akan kowace litar man fetur. kiddigar masana tattalin arziki, ta ce yanzu kowace litar man fetur kan shigo kasar nan akan N74.35, inda akan yi mata dawainiyar rabawa cikin kasa ta N15.49, jimla za ta tashi akan N89.84, don haka akwai sassaucin N2.84k, akan kowace lita ke nan, mu kuma muna amfani da lita miliyan 40 a kullum, wanda zai baka sassaucin N113miliyan a kullum, a wata zai kai N3.4biliyan, ya yin da a shekara ya doshi N40.8 biliyan.
Ragin, ya zo a daidai lokacin da `yan kasa suke kokawa da kuncin rayuwa. Abin tambaya shi ne ko ragin zai taimaka a samu saukin? Amsa, da kyar za a samu, bisa la`akari da irin yadda faduwar farashin man ta kawo karewar darajar musayar kudadenmu irin su Naira. Ya zuwa karshen makon jiya ana canjar Dalar Amurka daya akan N205, sabanin kafin faduwar, da canjin bai wuce N185, akan kowace Dala. Bisa ga la`akari da komai na tattlin arzkinmu ya ta`allaka ne akan kayayyakin da muke sawo wa daga kasashen waje walau don amfanin yau da kullum, ko don sarrafawa a Masana`antun mu, da wannan ke nan ina rayuwa za ta yi saukin ga Talakan kasar nan. Dadin-dadawa kuma gwamnati ta yi gum akan samun sassauci akan man gas da na bulak oyel, wadanda su Masana`atu suka fi amfani da su wajen tafiyar da Na`urorin Masana`antunsu. Sai dai mu ce Allah Ya kawo mana dauki.