Rago da akuya

Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya karatu? Tare da fatar ana lafiya kuma ana dada himma a makaranta. A yau na kawo muku labarin ‘Rago da akuya’. Labarin ya yi nuni ne ga yadda rashin rabon fada ke janyo sanadin wani ya ji ciwo. A sha karatu lafiya:   An yi wani rago mai manyan kaho. […]

Rago da akuya

Rago da akuya

Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya karatu? Tare da fatar ana lafiya kuma ana dada himma a makaranta. A yau na kawo muku labarin ‘Rago da akuya’. Labarin ya yi nuni ne ga yadda rashin rabon fada ke janyo sanadin wani ya ji ciwo. A sha karatu lafiya:

 

An yi wani rago mai manyan kaho. Ga shi yana ji da karfi don haka, ba kowane rago ke zuwa ya tunkare shi da komai ba, ballantana wajen karo. Kasancewar ya san sauran dabbobin na jin tsoronsa, haka ya sanya ya kebe wani katafaren fili inda ke da ciyawa koriya domin kiwo. Duk wanda ragon ya kama a wannan bangare sai ya illatar da shi.

Ran nan yana cikin bushasharsa a wannan bangare da ya ware wa kansa, sai ya ga akuya da ’ya’yanta suna kiwo a wannan waje da ya hana kowa zuwa kiwo.

Hakan ya bata wa rago rai matuka. Kawai sai ya tunkare akuya da fada ba tare da sauraren akuya ba.

A lokacin da ragon da akuya ke fada, akwai wani zomo da yake jin dadin kallon fadan da suke yi. Maimakon ya raba fadan, sai ya shiga tafi yana shewa har sai da rago ya karya kafar akuya.

Ganin akuya ta sha da kyar sai dabbobin dajin suka kai akuya zuwa asibiti. Likita na ganin wannan karaya sai ya ce babu abin da ya kamata a yi amfani da shi a dinke kafar akuya da ita face jijiyar zomo.

Haka aka kama zomo da karfin tsiya aka kayar da shi za a yanka shi a cire jijiyarsa. A lokacin ne ya yi da ya sani da ya raba fadan, tunda ga shi yanzu fadan zai yi sanadiyar rasa ransa.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos