Ragona yana bi na ko’ina saboda shakuwa – Salisu Direba

Wani matashin direba dan shekara 31 da ke a tashar ’Yan Kaba ta birnin Kano, ya bayyana yadda shakuwarsa da sabon da ya yi da ragonsa, ya sanya ragon yake biye da shi ko’ina ya shiga. Haka nan Salisu ya bayyana wa Aminiya cewa  yana da mata biyu da ‘ya’ya hudu. Ya kuma ce ya […]

Ragona yana bi na ko’ina saboda shakuwa – Salisu Direba
Ragona yana bi na ko’ina saboda shakuwa – Salisu Direba

Wani matashin direba dan shekara 31 da ke a tashar ’Yan Kaba ta birnin Kano, ya bayyana yadda shakuwarsa da sabon da ya yi da ragonsa, ya sanya ragon yake biye da shi ko’ina ya shiga. Haka nan Salisu ya bayyana wa Aminiya cewa  yana da mata biyu da ‘ya’ya hudu. Ya kuma ce ya yi shekara 12 yanzu yana aikin tukin mota daga Kano zuwa Nguru zuwa Gashuwa a Jihar Yobe, sannan ya ce yana zaune ne a Larabar Abasawa da ke karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.
Ya kuma ce duk inda sana’ar tukin motar da yake yi, shi mutum ne mai sha’awar kiwo. Ya ce “ni ma’abocin kiwo ne, ina kiwon dabbobi zuwa kaji zuwa zabi zuwa tantabaru, duk ina kiwata su.”  Ya kara da cewa ba wannan ragon ne kadai ya taba sabawa da shi ba daga cikin abubuwan da yake kiwo, domin ya ce a shekarun baya ma akwai akuyar da ya shaku da ita ita ma ta rika binsa duk inda ya shiga.
Da Aminiya ta tuntube shi kan dalilin shakuwarsa da dabbobi, sai  ya ce: “Ba wani abu ne ya san hakan ba, illa kula da abinci da nake bai wa dabbobin nawa, shi ya sa muke sabawa da su haka.” Ya kuma ce ita ma wannan akuyar da suka saba har yanzu tana nan bai yanka ta ko ya sayar da ita ba. Kuma ya ce duk da wannan ragon bai wuce wata daya da ’yan kwanaki ba, da ya sayo shi daga Jihar Yobe.
Malam Salisu ya ce duk da sabon da suka yi da ragon nasa, idan aikin tuki ya kama shi zai hau motarsa, yakan bar ragon ne a gida. Ya ce “ amma idan ina gida ba zan fita aikin tuki ba, shi ne nakan fito tare da ragon, saboda idan na bar shi a gida zai yi ta koke-koke.”
Sannan ya ce shi ma haka nan ba ya jin dadi idan ya fita ba tare da ragon nasa yana biye da shi ba. Sai dai kuma idan zai shiga wadansu wurare kamar kanti ko wajen da zai sayi abinci ko wajen da za a yi masa aski, ko kuma wajen da zai gana da wasu mutane, sai yakan bar ragon a kofa, shi kuma ya shiga wajen da ya je.
Ya ce, “idan ka ga na fito da ragona da ma irin wadannan abubuwan ban tanadi yin su ba kwata kwata.”
“Sirrin halayyar dabbobi ga masu kiwonsu,” a cewar Malam Salisu ya ce “su dabbobi bukatarsu kawai ta abinci ce, duk abin da dabba take so ka ba ta, ta ci ta koshi, idan ruwa take so ka ba ta, ta sha, in sha Allahu za ku yi saboda dabba.”  
“Babu wani asirin da yake da shi na jan hankalin dabba da ya wuce abinci,” inji shi.
A cewarsa, duk sabon da ya yi da ragon idan ya samu mai saye, kuma ya ga ya samu riba, kamar yanzu da sallar layya take karatowa, to zai sayar da shi, domin ya ce kafin wannan ragon ma ya sayar da wasu dabbobin da ya shaku da su.
 “Duk da haka nakan ji ba dadi a duk lokacin da na rabu da dabbar da na shaku da ita,” inji Salisu.
Jama’ ar kuwa kowa sai mamaki da sha’ awar yadda ragon nan yake bin Salisu direba yake yi, tare da yin magana a kan al’amarin.