Rahama Sadau ce mace mafi tashe a Najeriya a 2020 —Google

’Yan Najeriya sun fi neman Rahama, Aisha Yesufu da Maryam Sanda a Google a 2020

Rahama Sadau ce mace mafi tashe a Najeriya a 2020 —Google

Rahama Sadau

Jarumar masana’antar fim ta Kannywood, Rahama Sadau ce mafi tashe a cikin taurarun masana’antar da ma daukacin Najeriya a Google a shekarar 2020.

Sunan Rahama Sadau kadai ne daga Kannywood ya samu fitowa a jerin mutane da abubuwa 10 da aka fi nema a Google daga Najeriya a 2020.

Ita ce kuma macen da ta fi fice a Najeriya a jerin mutun 10 da jama’a suka fi neman bayanai a kansu daga kasar a shekarar.

Hakan nan kunshe ne a rahoton da kamfanin ya fitar kan abubuwan da al’ummar duniya suka fi sha’awar samun bayanai a kansu a shekarar.

Rahoton ya nuna Rahama ce ta fi tashe daga Arewacin Najeriya a shekarar, sannan Maryam Sanda – kowacce daga cikinsu labaranta sun karade shafukan zumunta a shekarar.

 

Mutum 10 mafiya tashe a Najeriya a Google a 2020

  1. Joe Biden
  2. Rema
  3. Naira Marley
  4. Rahama Sadau
  5. Hushpuppi
  6. Laycon
  7. Kamala Harris
  8. Omah Lay
  9. Maryam Sanda
  10. Kai Havertz

 

Tashen Rahama da Maryam Sanda a 2020

A baya-bayan nan ce-ce-ku-ce ya barke a shafukan zumunta bayan batancin da wani ya yi kan hoton da jarumar ta wallafa a Twitter.

Daga baya jarumar ta fito ta nesanta kanta da batancin tare da bayyana nadamarta kan yadda batancin ya samu alaka da hoton da ta wallafa, wanda tun a lokacin ta goge shi.

Ita kuma Maryam Sanda, a shekarar an yi ta tsokaci a kan sha’aninta bayan ba Babbar Kotun Tarayya ta yanke mata hukuncin kisa bisa zargin kashe mijinta a 2017.

Bayan ta daukaka kara, a baya-bayan nan Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da hukuncin da waccan kotun ta yanke mata.

Yanzu dai Maryam Sanda ta daukaka kara zuwa Kotun Koli.

 

Abuwan da aka fi nema a Google a 2020

Alkaluman da Google ya fitar sun nuna annobar coronavirus ce aka fi neman bayani a kanta a Google a shekarar 2020 a fadin duniya.

Rahoton ya nuna a shekarar, baya ga kalmar coronavirus, mutane sun fi neman bayani kan yadda ake hada sanadarin tsaftace hannu (hand sanitizer a Turance); sai alkaluman cutar da kuma alamominta.

Duk da yadda annobar ta buwayi duniya, abubuwan da ’yan Najeriya suka fi dubawa a Google a shekarar sun danganci fina-finai, wake-wake, shirye-shiryen talabijin, abinci, fitattun mutane da kuma zaben Shugaban Kasar Amurka.

A Najeriya, baya ga coronavirus, abubuwan da aka fi neman bayanai a kansu a Google sun hada zaben shugaban kasar Amurka, Shugaban Amurka Mai Jiran Gado, Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris, ASUU, Google Cla jaruma Rahama Sadau, Maryam Sanda, Aisha Yesufu, Hushpuppi, da kuma da mawaka irinsu Naira Marley, Davido da Simi.

 

Maudu’ai 10 mafiya tashe a Nejeriya (2020)

  1. Coronavirus
  2. US election
  3. Joe Biden
  4. Google Classroom
  5. ASUU
  6. Zoom Live
  7. Rema
  8. Naira Marley
  9. Rahama Sadau
  10. Hushpuppi

 

Wakoki 10 mafiya tashe

  1. Davido – Fem
  2. Simi – Duduke
  3. XXXTentacion – Bad
  4. Mayorkun ft Davido – Betty Butter
  5. Rema- Ginger me
  6. Rema – Woman
  7. Burna Boy – Wonderful
  8. Patoranking – Abule
  9. Naira Marley – Tesumole
  10. Davido ft Nicki Minaj – Holy Ground

 

Abinci mafiya tashe a Najeriya a 2020

  1. Pornstar martini
  2. Puff puff (fanke)
  3. Red velvet cake recipe
  4. Meat pie
  5. Chin chin
  6. Burodi
  7. Chocolate cake
  8. Miyar Oha
  9. Miyar Egusi

 

Tambayoyin da ’yan Najeriya suka fi yi

  1. Wane ne Shugaban Kasar Amurka?
  2. Yaushe za a bude makarantu a Najeriya?
  3. Yadda aka hada sanadarin tsaftace hannu
  4. Wane ne George Floyd?
  5. Yadda ake yin kyallen rufe fuska
  6. Wane ne Joe Biden?
  7. Wane ne Laycon?
  8. Yadda ake yin kek
  9. Wace ce Aisha Yesufu?
  10. Yadda ake yin burodi

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya