Rainin wayo
Wani dan tasi ne ya dauko wani Bature daga ofis, suna cikin tafiya sai suka biyo ta wani dogon bene kerarre, ginin ya yi kyau sosai. Baturen dama ya iya Hausa, sai ya ce wa direban: “Kai! Ginin nan ya yi kyau, a kwana nawa aka gina shi? Sai direban ya gyara zama, ya ji […]
Wani dan tasi ne ya dauko wani Bature daga ofis, suna cikin tafiya sai suka biyo ta wani dogon bene kerarre, ginin ya yi kyau sosai. Baturen dama ya iya Hausa, sai ya ce wa direban: “Kai! Ginin nan ya yi kyau, a kwana nawa aka gina shi? Sai direban ya gyara zama, ya ji an yabi abin kasarsu, ya ce: “Ai benen a shekaru biyu kacal aka yi aka kammala shi.” Bature ya yi tsaki ya ce: “A Amurka a wata shida za a gina ma wannan. Ku dai Afirika komai sai a hankali.” dan tasi ashe ya ji haushin Bature, suna biyo wani titi sai ga wani katafaren filin kwallon kafa na zamani, sai kuwa Bature ya kara tambayar lokacin da aka diba wajen gina shi. Shi kuwa sai ya ce: “To ni dai dazu da na wuce babu wannan sitadiyam amma yanzu ga shi har an gina shi. Ina ganin dazu da safe aka gina shi. Sai Bature ya juyo da dan Turancinsa a fusace ya ce: “Hey! Ka ga malam, kar ka raina mini hankali. Ya za ka ce a rana daya aka gina sitadiyam? To ko mu a can Turai ana daukar kamar shekaru biyu ko uku a gina!”
Daga Buhari Liman Kudan