Rainin wayo(1)
Rainin wayoWani dan tasi ne ya dauko wani Bature daga ofis, suna cikin tafiya sai suka biyo ta wani dogon bene kerarre. Ganin benen ya yi kyau, Baturen dama ya iya Hausa, sai ya ce wa direban: “Kai! Ginin nan ya yi kyau, a kwana nawa aka gina shi? Sai direban ya gyara zama, ya […]
Rainin wayo
Wani dan tasi ne ya dauko wani Bature daga ofis, suna cikin tafiya sai suka biyo ta wani dogon bene kerarre. Ganin benen ya yi kyau, Baturen dama ya iya Hausa, sai ya ce wa direban: “Kai! Ginin nan ya yi kyau, a kwana nawa aka gina shi? Sai direban ya gyara zama, ya ji an yabi abin kasarsu, ya ce: “Ai benen a shekara biyu kacal aka yi aka kammala shi.” Bature ya yi tsaki ya ce: “A Amurka a wata shida za a gina ma wannan. Ku dai Afirka komai sai a hankali.” dan tasi ashe ya ji haushin Bature, suna biyo wani titi sai ga wani katafaren filin kwallon kafa na zamani, sai Baturen ya kara tambayar lokacin da aka diba wajen gina shi. Shi kuwa sai ya ce: “To ni dai dazu da na wuce babu wannan sitadiyam amma yanzu ga shi har an gina shi. Ina ganin dazu da safe aka gina shi. Sai Bature ya juyo da dan Turancinsa a fusace ya ce: “Hey! Ka ga Malam, kada ka raina mini hankali. Yaya za ka ce a rana daya aka gina sitadiyam? To ko mu a can Turai ana daukar kamar shekara biyu ko uku ana gina shi!”
Daga Buhari Liman, Kudan
Gasar gudu
Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, ran nan ya tafi wurin aiki, inda ya kai kilomita 25. Ya yi tafiyar da ta kai kilomita 23, saura kilomita biyu ya isa, kawai sai suka yi kiliya da wani matashi, shi ma yana tika gudu a nasa babur din. Yana ganin wannan matashi da yake gudu, kawai sai ya yi kwana ya bi shi. Da wancan ya waigo ya ga an biyo shi da gudu, sai ya kara wuta, domin bai son a wuce shi. Nan fa suka runtuma, suka yi ta gasar tsere a tsakaninsu. Sai da suka ci kilomita 20, sannan ya samu wuce shi, daga nan ya juyo domin tafiya wajen aikinsa. Ya ce: “Haba, ai da ban wuce shi ba, sai ya yi ta kurin shi mai gudu ne.”
Sunusi Uban Kulob, Garko Kano 07038766018
Keken Banufe
Wani manomi Banufe ne tare da dansa suna aiki a gona. Da ya ga gyadarsa ta yi kyau sosai, sai ya ce wa babban dansa: “Bana zan sayi keke.” dansa sai ya ce: “Ni kuwa zan kada karaurawa ke nan.” Jin haka sai baban ya kai masa mari, ya ce masa: “Kana son ka bata keken ne?”
Daga 08032859794