Rajistar katin dan kasa ta zama alakakai a Kaduna

Shirin yin rajistar katin dan kasa (e-ID Card) da aka fara a Jihar Kaduna ya fara da kafar hagu, sakamakon karancin kayan aiki, inda hakan ya ya janyo yin rajistan ya zamo sai mai karfi.Wakilinmu wanda ya ziyarci Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Kawo ya iske cincirindon jama’a, kuma mutane da dama sun ce tun […]

Rajistar katin dan kasa ta zama alakakai a Kaduna
Rajistar katin dan kasa ta zama alakakai a Kaduna

Shirin yin rajistar katin dan kasa (e-ID Card) da aka fara a Jihar Kaduna ya fara da kafar hagu, sakamakon karancin kayan aiki, inda hakan ya ya janyo yin rajistan ya zamo sai mai karfi.
Wakilinmu wanda ya ziyarci Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Kawo ya iske cincirindon jama’a, kuma mutane da dama sun ce tun karfe 5:00 na asuba suke zuwa don eman katin dan kasar.
Sun ce bayan karfe 8:00 na safe ta yi sai su yi layi a ofishin da ake daukar hoto a kwamfuta da ba su da yawa, bayan nan sai a ce mutum ya dawo ya karbi takardar shaidar bayan mako guda, kafin ya yi ta jiran gawon-shanu don karbar katin dindindin.
Muhammad Bashir Adam, mazauninTudun Wada a yankin Kaduna ta Kudu, da Aminiya ta iske a wurin yin katin a fusace, ya ce shirin ya zama shirme don ya kamata ne a bi jama’a unguwannnisu a yi musu katin. Ya ce ya je yin katin ne tun karfe 9:00 na safe, amma da karfe 12:00 ta yi sai aka ce musu an tashi, bayan an dauki mutum 80 daga cikin 200 da suke layi.
Alhaji Yusuf Tsiga Tafidan Unguwar Kanawa Kaduna cewa ya yi, ana yin Sallar Asuba ya je don bin layi, amma sai da karfe 12 ta gota sannan aka yi masa, yayin da wata budurwa mai suna Fatima Umar ta ce ta je da karfe 6:00 na safe kuma an yi mata da 3:30 na yamma.
Bincike ya nuna cewa lokacin da sabon kati ya fara aiki gadan-gadan, tsohon katin dan kasa da ake amfani da shi yanzu, zai zama tarihi.
Sannan wanda za a yi masa katin sai yana da tsohon katin ko lasisin tukin mota ko fasfo ko takardar shaida daga mai unguwarsu.
Hukumar Rajistar ’Yan Kasa (NIMC) ta ki amsa sakon da waya da wakilinmu ya aike mata kan yadda aikin rajistar ke da wuya saboda karancin kayan aiki.