Rakumi ya tare a kabarin maigidansa

Wani rakumi a wani kauye da ke kasar Yemen ya tare a kabarin maigidansa, har tsawon kwana shida da rasuwarsa. Wadanda wannan al’amari ya auku a gabansu, a kauiyen Sidah da ke gundumar Ibb, sun bayyana cewa rakumin ya halarci jana’izar maigidansa, marigyai Ali Al Na’ana sannan ya ki barin wurin har masu zaman makoki […]

Rakumi ya tare a kabarin maigidansa
Rakumi ya tare a kabarin maigidansa

Wani rakumi a wani kauye da ke kasar Yemen ya tare a kabarin maigidansa, har tsawon kwana shida da rasuwarsa. Wadanda wannan al’amari ya auku a gabansu, a kauiyen Sidah da ke gundumar Ibb, sun bayyana cewa rakumin ya halarci jana’izar maigidansa, marigyai Ali Al Na’ana sannan ya ki barin wurin har masu zaman makoki suka tashi, kamar yadda jaridar Gulfnews ta ruwaito.

Al Wajeeh Ali, wani mazaunin kauyen, wanda ya baza labarin rakumin, ya ce, dan marigayi Al Na’ana ya janye rakumin daga makabartar don gudun kada a sace shi, amma da komawarsu gida sai ya koma kusa da kabarin marigayin yana sansanashi.
Mazaunan yankin sun ce, wannan rakumi da ke alhinin rasuwar maigidansa ya tare a makabarta har tsawon mako guda. Kuma duk sa’adda iyalan mamacin suka matsa wa rakumin ya koma gida, sai ya dawo daga bisani.
Ali ya bayyana wa jaridar gulfnews cewa duk sa’adda rakumin ya kusanci kabarin sai kawai ya yi ta sansanashi, sannan ya zauna a wurin. “Wannan kabari ya zama wurin ziyara ga dimbin mutane,” inji shi.
Ali ya ce mutane da dama daga yankin tekun Fasha sun bijiro da bukatar jneman a sayar musu da rakumin. Rakumin dai ya ki ci, ya ki sha,” inji shi.