Rakumin Buzu 03

Wani Buzu ne bai taba zuwa birni ba sai abokansa suka ce masa ya shirya su je birni. Suna tafiya a kan rakuma sai mota ta wuce, kafin ya ankara ta bace. Sai ya tambayi wani daga cikinsu cewa wane irin mai ake zuba mata take gudu haka? Aka gaya masa cewa wani irin mai […]

Rakumin Buzu 03
Rakumin Buzu 03

Wani Buzu ne bai taba zuwa birni ba sai abokansa suka ce masa ya shirya su je birni. Suna tafiya a kan rakuma sai mota ta wuce, kafin ya ankara ta bace. Sai ya tambayi wani daga cikinsu cewa wane irin mai ake zuba mata take gudu haka? Aka gaya masa cewa wani irin mai ne idan muka je zai nuna masa. Da suka isa masauki aka daure rakuma sai abokinsa ya ja hannunsa suka shiga gari. Da zuwansu sai ya nuna masa gidan mai, shi kuwa ya je ya taho da rakumisa; ya je ya samu mai ba da mai ya tambaye shi cewa: “Rakumi zai sha lita nawa?” Mai ba da mai ya ce: “A ina za a zuba?” Ya ce a duburar rakumin. Ya ce masa ai ba a zuba wa rakumi mai. Buzu ya ce: “Kar ka raina mini hankali!” Nan aka daga jelar rakumi aka matsa masa fetur. Da rakumi ya ji sabon abu a cikinsa, sai ya kwace daga hunun Buzu, ya fita da gudu, ya yi arewa. Buzu ya yi ta yi wa rakumi tsawa don ya tsawa amma ya ki tsayawa. Buzu kwabe wandonsa ya ce wa mai sayar da mai: “Zuba mini lita biyu in bi rakumina.” Daga Azzubair M. Fagge