Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata
Ramadana watan ibada ne da neman kusancin Allah da tsarkake ruhi.

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ina mana lale barka da zuwan masoyi watan Ramadan. Da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkan alheran da ke cikinsa kuma Ya sa mu zama daga cikin ’yantattun bayinsa, amin.
Ramadan: Alherai goma ga Ma’aurata.
1. Gyaran aure:
Ramadan lokaci ne na ibada da kyautata ibada. Aure da zamantakewar aure yana ɗaya daga cikin manyan ibadojin Addinin Musulunci.
A wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah Sallalahu Alayhi wa Sallam Yace, Aure rabin Addini ne. Don haka kamar yadda muke dagewa wajen ayyukan addini da gyaran alakar mu da Allah, to ya kamata ma’aurata suyi amfani da Ramadan wajen gyaran alakar su da inganta zamantakewar tsakaninsu.
Bayan dagewa wajen ayyukan ibada irinsu Sallah cikin lokaci, karatun Alkur’ani, tarawiy da sauransu, to sai a dubi wasu wajibbun ayyuka zaman aure su a ingantasu, a kyautata su, waɗanda aka mance ba a yi a farfaɗo da su.
Haka kuma yadda muke yawan istighfāri cikin Ramadan da komawa ga Allah cikin tuba da neman yafiyar ayyukanmu na zunubi, to haka ya kamata ma’aurata su koma ga abokin aurensu, su tunano abubuwan da suka aikata na rashin kyautatawa da ba daidai ba da ganganci ko bisa kuskure, su basu hakuri kuma su nemi yafiya da gafararsu. Sannan su juya cikin kawunansu, su duba su gani meye abokin aurensu ya yi musu na laifi bisa kuskure ko da ganganci da kyautata niyya su yafe masu, wannan laifin su share shi da zuciya da ma’aikatar hankalinsu.
Duk Ma’auratan da suka aikata haka za su ji wata sabuwar iska mai daɗi tana ratsawa cikin rayuwar aurensu. Wannan zai sa ayyukan ibada su zama masu sauki da daɗin aikatarwa garesu. Sakamakon hakan shi ne more ma jiga-jigen alherai guda biyu, na watan Ramadan da kuma na ibadar aure.
2. Ibadar aure:
An san watan Ramadana watan ibada da neman kusancin Allah da tsarkake ruhi.
Abinda ba a cika ba muhimmanci shi ne alakanta watan Ramadan a matsayin watan assasa da inganta ibadar aure. In mun lura, a cikin Alkur’ani, bayan Allah Maɗaukakin Sarki ya yi magana akan Ramadan, aya mai bi mata sai tayi magana akan addu’a.
Aya mai bi mata sai ta yi magana: An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima’i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah Yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, za su yi taƙawa. -Aya ta 187, Suratul Bakarah Wannan aya ta bayyana muhimmancin ibadar aure a tsakanin Ma’aurata, don haka yakamata ma’aurata su assasa wannan ibada tare da sauran ibadojinsu a cikin wannan wata mai alfarma.
Mu sani cewa azumi yana wanke hanyoyin jini, yana kauda dattin na’urorin kwakwalwa, kuma yana gyara manyan namomin jiki, ciki har da na’urorin sha’awa.
Sannan canjin yanayin abinci ta hanyar yawan kayan marmari da ganyayyaki shi ma wani al’amari da ke taimaka wa ma’aikatar sha’awa. Don haka ma’aurata suyi amfani fa ɗimbin damarmaki wajen assasa da zafafa ibadar aurensu cikin Ramadan.
3.Tahaddu Tahabbu
Manzon Allah Sallalahu Alayhi wa Sallam Ya ce: Ku yi musayar kyaututtuka tsakaninku, sai ku so junanku. Wannan wata kyakykyawar Sunnah ce da ya kamata ma’aurata su assata cikin wannan wata na Ramadan don karin dankon so da kauna a cikin rayuwar aure.
Ba dole sai abu mai tsada ba, kawai ’yan ƙananan abubuwa da za su sa abokin aure ya ji, shi na musamman ne, za su sa yaji ai ana ji da shi ko ita.
Misali kamar maigida ya sayowa uwargida wata irin cakwalet mai daɗi koda kwaya ɗaya ce, ko uwargida ta shirya wani girki na musamman daga aljihunta don mijinta, abinda ta san yana matukar so koda kwaɗon rama ne ko rummace.
Sai mako na gaba in sha Allah da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a ko yaushe