Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata

Maimakon Maigida ya yi tasbihi da yatsunshi, yana iya yi da yatsun matarsa, ita ma haka.

Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Ga ci gaban bayani kan alherai goma ga ma’aurata cikin Ramadan.

4. Salon buɗa baki

Ma’aurata za su yi amfani da lokacin buɗa baki don ƙara kusanci, farfaɗo da shau’uka cikin zuciya da ɗumama sha’awa.

Ma’aurata su tsara buɗa bakinsu ta yadda za su zama kamar dai su sabbin masoya ne da suka sami kansu tsundum cikin sabuwar soyayyar juna.

Suna buɗa bakin cikin wasa da raha da tsokanar juna, ciyar da juna a baki, kallon marmasa soyayya da kiran juna sunayen soyayya masu ƙayatarwa da sa nishaɗi.

5.Wasanni:

Don ɗebe ma juna kewa lokacin azumi, ta hanyar wasanni na baka, na jiki da kuma na wasa kwakwalwa.

Misali da Yamma lokacin da uwargida ke kakaniyar aikin gida, Maigida da iya ɗebe mata kewa da wannan wasan kacici kacicin: maigida zai ce da uwargida na fi son ki saboda kaza da kaza. Ita ma sai ta ba shi amsa, a’a nice dai na fi son ka saboda kaza da kaza.

Haka za su yi tayi wanda dalilai suka ƙare masa shi ya faɗi wasan. Bayan buɗa baku kafin lokacin tarawiyyi wasan tsere, ko tsalle ko kuma wanda yafi dace.

A kwanakin karshen mako kuma Ma’aurata su shirya ma juna kacici kacici akan wani ɓangare na ilmi, kamar akan Ramadan, Kur’ani ko tarihin Annabi Sallalahu Alayhi wa Sallam. Wanda ya ci kuma a gabatar da wata ’yar kyauta gare shi.

Waɗannan wasanni suna da matukar muhimmanci da kara karfin igiyar auren, minti goma ya yi yawa wajen aikantar da su, amma za su bar farin ciki na har abada a zuciyar Ma’aurata.

6.Ɗauke nauyi:

A dubi wani abu mai nauyi ga abokin aure sai a sauke masa wannan nauyin dan ya ji saukin Ramadan kuma a sami lada mai yawa.

Kamar wata rana Maigida ya ce uwargida ta huta, ya je ya haɗo kayan buɗa baki gaba ɗaya daga waje sai dai a zuba a ciki. Ko in uwargida ta kwashi adashenta ta canza su zuwa sababbin kuɗi ta sa ambulan ta ba Maigida ta ce ga shi ya ƙara na hidimar azumi da Sallah.

Ma’aurata dai su dubi abinda ya nauyaya ga abokin aurensu wanda sauke sa zai kawo masu saukin rayuwa sai su sauke ma shi daidai iyawarsu.

7.Sadaukarwa

Shi ne Ma’aurata su sadaukar da wani abu daga rayuwarsu dan kyautatawa ga abokin aurensu.

Kyakykyawan zamantakewar aure itace mai cike da yawan sadaukarwa ta kowane ɓangare.

Don dacewa da nun’in ladar da ke cikin Ramadan, Ma’aurata sai su aikatar da ayyukan sadaukarwa ga junansu.

Kamar maigida ya rika taya uwargida aikin gida ko ta fannin wanki da gugar kayan yara ne kawai.

Yana daga cikin Sadaukarwa kau da kai daga abubuwa marasa daďi ta ɓangaren abokin aure, kar a zarge shi game da nakasun sa da kuma yafe ma kurakurensa

8.Tunatarwa:

Sai Ma’aurata su yi nazari kan wani rauni na junansu ta ɓangaren Addini, hallayya da zamantakewa, musamman in wannan rauni da zai haifar masu da matsala a ranar hisabi, kamar rashin yin Sallah cikin lokaci, kamar yawo da zancen mutane, kamar rashin zuwa masallaci ga maigida da sauransu.

Sai a shirya nasiha da tunatarwa mai ratsa zuciya ga abokin aure akan wannan rauni nasa.

A rika nuna masa illolinsa da kuma irin halakar da za su auka da shi tun a duniya da kuma lahira.

Wannan tunatarwar za a yi ta da kalamin baki, a rubuce a takarda ko a sakon wayar tafi da gidanka.

A lura ban da zargi da ɗora laifi a cikin nasiha sai dai faɗakarwa da nusantarwa.

9.Romansiyya:

Misalan abubuwan romansiyya da Ma’aurata za su iya yi cikin Ramadan, in uwargida tana sanwa a kichin maigida ya lallaɓa ya rufe mata ido ta baya, uwargida ta rubuta wasikar soyayya ta sa a ma’ajiyar kuɗin mijinta ko a aljhunsa sai ya tafi wajen aiki ya fito da ita ya karanta.

Bayani mai lamba 5 shi ma ya shigo cikin ayyukan Romansiyya musamman wasan ‘na fi son ki saboda kaza’

10. Yin ibada tare:

Wannan shi ne mafi muhimmanci a cikin abubuwa goman da suka gabata. Ma’aurata su rika neman kusancin Allah ta hanyar yin ibadojinsu tare duk lokacin da yin hakan ta kama kuma suna waje ɗaya.

Maimakon Maigida ya yi tasbihi da yatsunshi, yana iya yi da yatsun matarsa, ita ma haka. Yin musafar Al-Qur’ani tare, ko ɗaya ya karanta ɗaya ya karanta fassarar Ayoyin.

Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko yaushe, amin.

Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano

Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP

Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata