Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe
Ɗan majalisar ya ce rabon wani ɓangare ne na rage wa jama’a raɗaɗi a watan Ramadan.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga/Billiri a Jihar Gombe, Ali Isa JC, ya raba wa Musulmai da Kiristoci 2,000 kayan abinci don rage wahalar Azumin watan Ramadan da na Kiristoci.
Ali JC ya bayyana cewa wannan tallafi yana da muhimmanci don sauƙaƙa wa jama’a gudanar da ibadarsu cikin sauƙi.
- An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba
- WHO za ta bai wa Nijeriya magungunan cutar kuturta
“Buƙatar kayan abinci tana ƙaruwar a irin wannan lokaci, kuma muna ƙoƙarin taimaka wa mutanen mazaɓarmu su samu sauƙin rayuwa,” in ji shi.
Baya ga kayan abinci, ya kuma raba babura 10 da babura masu kafa uku guda 20 domin tallafa wa mutane 200 a Jihar Gombe, inda kashi 50 cikin 100 aka ware wa mazaɓarsa.
Ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su kasance masu godiya, su yi addu’a domin zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
A gefe guda, ya bayyana cewa yana da muhimmanci a bar kotu ta yi aikinta kan cece-kucen da ke tsakanin Sanata Natasha Akpoti da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
“Dole ne mu bari doka ta yi aikinta ba tare da son zuciya ba,” in ji shi.
Tallafin da Ali JC ya bayar yana cikin ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’ummarsa da kuma tallafa wa jama’a a Jihar Gombe.