Ramadan: An ba makarantun Kano hutun azumi
An ba makarantu hutun mako biyar domin dalibai su yi azumin Ramadan a gida.
Gwamnatin Jihar Kano ta rage tsawon zangon karatun da dalibanta ke ciki domin ba su hutun su yi azumin watan Ramadan a gida.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa’id, ya sanar da cire mako daya daga zagon karatu na biyu ya koma mako 12, an kuma kara hutun zangon daga mako hudu zuwa mako biyar.
Sanarwar da Babban Sakataren Ma’aikatar, Aliyu Yusuf, ya fitar ta ce an sauya jadawalin karatun ne a sakamakon bukatar da iyayen daliabai da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar wa gwamnatin jihar na bai wa ’ya’yansu damar yin azumi a gida, lura da muhimmanci da kuma falalar watan Ramadan.
Ma’aikatar ilimin ta bukaci iyayen dalibai da su kasance masu lura da ’ya’yansu a tsawon lokacin hutun, musamman a wannan yanayi na matsalar tsaro.
Ta kuma shawarce su da su tabbata yaran suna yin abubuwan da za su amfane su a tsawon lokacin hutun.