Ramadan: An rage wa ma’aikatan Bauchi lokacin tashi daga aiki
Daga Litinin zuwa Alhamis ma’aikata za su riƙa tashi daga aiki da ƙarfe 3:00 na rana.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da rage wa ma’aikata lokutan aiki a fadin jihar albarkacin watan azumin Ramadan na bana.
Sanarwar na kunshe ne cikin wata takarda da aka fitar a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, mai ɗauke da sa hannun Daraktan Harkokin Ma’aikata a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Isma’il Ibn L. Garam.
- Ramadan: MDD ta bukaci al’ummar duniya su nuna tausayi da zaman lafiya
- ’Yan bindigar da suka sace matafiya 6 na neman fansar N100m a Benuwe
Takardar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa wa ma’aikatan Musulmi da kuma ba su damar samun isasshen lokacin gudanar da ibadu da sauran ayyukan alheri a cikin watan mai alfarma.
A cewar sanarwar, daga Litinin zuwa Alhamis ma’aikata za su riƙa tashi aiki da ƙarfe 3:00 na rana, yayin da ranar Juma’a za a ci gaba da tashi daga aiki da ƙarfe 1:00 na rana kamar yadda aka saba.
Haka kuma, an buƙaci ma’aikata da su yi amfani da watan Ramadan wajen yi wa jihar Bauchi da Nijeriya baki ɗaya addu’ar zaman lafiya, ci gaba da haɗin kai.
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan tsari zai fara aiki ne daga farkon watan Ramadan har zuwa ƙarshensa.