Ramadan: An sassauta dokar hana fita a Yobe

Mai bai wa Gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wani taron tsaro da mataimakin Gwamnan jihar Hon. Idi Barde Gubana ya jagoranta.

Ramadan: An sassauta dokar hana fita a Yobe

Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗage dokar hana fita na tsakar dare domin bai wa mazauna yankin musamman Musulmi damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali ba tare da takura ba.

Mai bai wa Gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wani taron tsaro da mataimakin Gwamnan jihar Hon. Idi Barde Gubana ya jagoranta.

Abdulsalam ya ce,  kwamitin tsaro na jihar ya ɗauki matakin da ya dace don bai wa Musulmi damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali a lokacin azumi.

Ya bayyana cewa, majalisar ta duba yanayin tsaro a faɗin jihar tare da ƙuduri aniyar ƙarfafa matakan kariya a duk tsawon watan Ramadan.

A cewarsa, watan Ramadan yana da ayyuka daban-daban na addini da suka haɗa da wa’azi, tarurrukan ƙarawa juna sani, sallolin jam’i, buɗa baki da kuma ƙiyamul Lail, waɗanda da yawa daga cikinsu sukan kai dare kuma suna buƙatar kasancewar jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa, an kira taron tsaron ne domin tantancewa da kuma nazarin yanayin tsaro a faɗin jihar da kuma tabbatar da ganin ’yan ƙasa sun gudanar da ibadun kwanaki 30 na watan Ramadan cikin kwanciyar hankali, tare da kare rayuka da dukiyoyin su yadda ya kamata.

Mai bai wa Gwamnan shawara kan harkokin tsaron ya ci gaba da bayanin cewa, a irin waɗannan lokuta, wasu masu aikata laifuka na iya yunƙurin yin aikata haramtattun ayyuka.

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da tallafawa jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihin bayanai domin ɗorewar zaman lafiya da ake samu a jihar.

Tags