Ramadan: N1.5bn muka fitar domin ciyarwa a Kano — Abba

Gwamnan ya musanta rade-radin da ake na cewar gwamnatinsa ta ware biliyan shida domin ciyar da mutane a jihar.

Ramadan: N1.5bn muka fitar domin ciyarwa a Kano — Abba

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusif, ya musanta zargin cewa gwamnatinsa ta ware Naira biliyan shida domin ciyar da al’ummar jihar a watan azumin Ramadan.

Gwamnan ya ce Naira biliyan 1.5 gwamnatinsa ta ware a matsayin kudin ciyarwa azumin bana.

Gwamnan ya bayyana hakan ne, cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“Ina so na shaida wa duniya cewa, ainihin kudin da gwamnatinmu za ta kashe Naira biliyan 1.5 ne gaba daya kwanakin Azumin”.

A cewar gwamnan bayanan da ke yawo a kafafen watsa labarai, babu gaskiya a cikinsu domin abin da aka bayyana ba haka suke ba.

Ya shawarci kafafen yada labarai da su rika tabbatar da kididdigar ayyukan gwamnati ta hanyar tuntubar madogara mai tushe domin kaucewa abin da gaskiya ba.

Sakataren gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa an raba kayayyakin ciyarwar zuwa cibiyoyi 100 a kananan hukumomin da ke cikin birnin jihar guda takwas, wanda za ake ciyar da mutum 1000 a kullum.

Ya jaddada cewa gwamnatinsu a tsaye take domin tabbatarwa abubuwa sun tafi daidai.

“Hakan ya sa gwamna da kansa ya kai ziyarar bazata Cibiyar Gidan Maza a Karamar Hukumar Birnin Kano guda takwas, inda ya nuna rashin gamsuwarsa game da irin abincin da ake dafa wa mabukata wanda ba shi da inganci sosai.

“Tuni gwamnan ya kafa kwamiti don tabbatar da an samun gyara a harkar gudanar da ciyarwar gaba daya.”

A cewarsa nan ba da jimawa gwamnatin Jihar tare da hadin kan kananan hukumomi sun sayo kayan abinci mota 132 na buhun shinkafa wanda za a raba a fadin kananan hukumomi 44 a lokacin azumi.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana